An cafke mutum 16 kan sayar da kananan yara a Gombe
Cikin wadanda ake zargi a badaƙalar sayar da yara har da jami’in gwamnatin Gombe
Wasu mutane 16 da ake zargi da sayar da kananan yara sun shiga hannun hukuma a Jihar Gombe.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce babbar wadda ake zargin an kama ta ne a unguwar Barunde da ke garin Gombe.
Jami’in ya ce mazauna unguwar Barunde ne tsegunta musu cewa matar na ajiye ’yan mata da suka yi ciki babu aure a wani gida suna rainon cikin, idan suka haihu masu gidan su karbi jaririn su sayar su sallami wadda ta haihun.
A cewar Mahid, wannan ba shi ne karon farko ba, dubun ta ne ya cika aka kama ta, don haka ya ke sanar da al’umma cewa su dinga sanar da hukuma motsin duk wani wanda basu yarda da shi ba.
- Kotu ta tsare Dan Bilki Kwamanda kan cin zarafin Kwankwaso
- DSS ta cafke Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Bello Bodejo
“Asirinsu ya tonu ne a lokacin da wani da ya yi wa wata ciki ta haihu aka bai wa wata jarirn bisa yarjejeniyar duk lokacin da ta bukacin ganin ’yar za ta gan ta.
“Sai aka dauki tsawon lokaci ba labari, a nan ne uwar ’yar ta yi bore ta sanar da wanda ya yi mata cikin ya tona asirinsu, aka gano irin aika-aikar da suke yi a wannan gida” in ji Mu’azu.
Da Aminiya ta ke zantawa da babbar wadda ake zargin a ofishin rundunar, ta ce ita ba ta sayar da yara, karbar yarinyar ta yi da nufin ta yi reno ganin tana sha’awar kananan yara, kasancewar tunda mijin ta ya rasu ba ta sake aure ba.
Ta ce saboda haka ne ta je Ofishin Kula da Walwalar Jama’a (Social Welfare) aka ba ta yarinyar tun tana makonni biyu a duniya, kuma yanzu ta kai shekara biyu tana tare da ita ba ta sayar ba; idan tana sayar da jarirai ai da sai ta sayar da ita ko ta sayar da ’ya’yanta da ta haifa.
“Wannan zargi sharri aka yi min domin tunda ubana ya haife ni ban taba sayar da yaro ba, da zan sayar ai da na sayar da wadda na karba tun farko,” in ji ta
Ta kara da cewa ganin ta samu Yarinyar a social welfare ne shi ne wata kwawarta ma ta yi sha’awar a ba ta “idan zan yi mata hanya ta samu tana so, shi ne fa na yi mata hanya aka ba ta.
“Jin dadin ta samu shi ne ta ce nawa ake biya? Na ce mata ba a bayar da kudi, kyauta suke bayarwa.
“Shi ne ta ce min tana son ta bayar da tukuici, kamar nawa za ta bayar, na ce duk abin da ta yi niya.
“Shi ne ta ce to za ta ba da wani abu, yaya za a yi a samu takardun mallakar jariri? Na ce kar ta damu zan karbo mata, jin haka sai ta ce na turo akawun namba za ta turo kudi na kai musu, shi ne na tura ta turo 400,000.
“Sai naje na cire kudi na kai musu domin sun ce kudi a hannu suke so, sai na ba su dubu 200,000 na dauki 200,000.
Ta yi kira ga rundunar ta ’yan sanda da cewa, yana da kyau idan za su yi aikinsu, su tsananta bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Shi ma jami’in social welfare din da ake zargin da hadin bakinsa a harkar, Haruna Abubakar, cewa ya yi ba shi da masaniya kan duk yaran da ake zargin mavar da sayarwa.
A cewarsa, yanzu da ’yan sanda suka kama ta ne ta ce musu a Social Welfare aka ba su yarinyar bayan ba su suka ba ta ba.
Ya ce shi dai yarinya daya ya sani sun taba ba ta da dadewa, ita ce wacce take rike da ita, bayan ita bai san wata ba, domin wacce asirin nasu ya tonu akanta DA’AWAH ne suka ba su ba social welfare ba.
A cewarsa, ta zo wajensu ne “tana son a yi musu takarda cewa Da’awah sun ba su yarinya amma babu takarda sai an zo Social Welfare.
Shi ne ya ce suje su kawo uwar yarinyar suka ce ta rasu, na ce to su kawo kakanta don mu tabbatar da kuma hoto su rubuta takarda wa Shugaban Karamar Hukumar Gombe cewa an ba su yarinya a Da’awah, tunda ba gwamnati ce ta ba su ba, za su yi raino sai su kai wa hakimin su ya sa hannu sannan su kawo musu.
A cewar Haruna, da ta zo wajen su ce musu ta yi yayarta za ta karba wa yarinyar saboda ba ta haihuwa kuma idan suka cika ka’ida za su ba su takarda.
Batun karbar kudi, ya ce shi bai san yadda suka yi ba, sai bayan sun ba ta takarda, “ashe wata mata daban ta kaiwa varinyar ba addarta ba, a wajen matar ta karbi kudi Naira 400,000.”
Ya kara da cewa, ba mu nemi kudi a wajenta ba domin ba sayar da yaran muke ba; Kakan yarinyar ne ya ce a ba shi wani abu shi ne suka ba shi dubu 80, sai suka tambaye ta sauran kudin fa sai ta ce su rike, wato 120,000 a zaman ta yi musu ihisani.
Shi ma yace ganin wannan shi ne karo na farko da ya taba shiga irin wannan matsala ya nemi a masa afuwa domin kuskure dai ya faru kuma shi ba aikin sa bane sayar da yara.