An kama mutum 6 da ke sayar wa masu garkuwa da mutane layin waya
An samu nasarar kama su ne tare da hadin kan jami’an hukumar leƙen asiri na SID.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta kama wasu mutum shida da ake zargi sun ƙware a sana’ar sayar da layin wayar salula wato sim card ga masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a babban birnin kasar.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Benneth Igweh ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai holen waɗanda ake zargin a ranar Alhamis.
- ’Yan sanda sun haramta Hawan Sallah a Kano
- Tinubu da Shettima sun kashe N5bn a tafiye-tafiye cikin watanni uku
Ya ce an samu nasarar kama su ne tare da hadin kan jami’an hukumar leƙen asiri na SID ƙarkashin jagorancin ACP Mohammed S Baba.
A cewarsa, waɗanda ake zargin sun kware wajen siyar wa miyagu layin wayar da aka riga aka yi wa wasu wadanda ba su ji ba su gani ba rijista.
Ya bayyana cewa ababen zargin suna mallakar layin wayar salular ne da shaidar wasu don gudun kada a gano su ko bin diddigin bayanansu.
Kazalika, ya ce suna sayar da layin wayar akan farashin N3,000 zuwa N5,000 ga kowane sim card daya.
“Akwai mamaki ganin cewa za a iya yin rajistar lambobi huɗu daban-daban a ƙarƙashin lambar dan kasa ta NIN guda ɗaya.
“Saboda haka, waɗannan miyagu suna ɗaukar masu siyar da layin a kan titi don samun cikakkun bayanai na mazauna da ba su ji ba ba su gani ba, waɗanda ke mallakar layin wayar bayan an yi musu rajista,” in ji shi.