An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa

An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris.

An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa

’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa.

An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba kaɗan.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Dankombo Morris, ya yaba wa jami’an da suka yi ruwa da tsaki wajen cafke ababen zargin, yana mai jaddada aniyar ƙara ƙaimi wajen tsare dukiyoyin al’umma.

Rundunar ’yan sandan ta buƙaci mazauna da su ci gaba da ba ta haɗin kai wajen lura da duk wani motsi tare da kai rahoto duk wani abin zargi zuwa mahukunta mafi kusa.