An cafke shugaban hukumar tabbatar da Ingancin kayayyaki na Kano

Ana zargin shugaban hukumar da karbar rashawa.

An cafke shugaban hukumar tabbatar da Ingancin kayayyaki na Kano

Zargin karbar rashawa ya sanya Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano (PCACC), cafke shugaban Hukumar Tabbatar da Ingancin Kayayyaki, Bello Alkarya.

Da yake tabbatar da kamun, shugaban hukumar, Barista Mahmud Balarabe, ya ce an cafke Alkarya ne bayan samun sa da laifin karbar cin hanci.

“Yanzu haka yana tsare a wajenmu bayan samun shi da laifi. Ana gudanar da bincike kuma zai ci gaba da zama a hannunmu,” a cewar Balarabe.

Idan ba a manta ba, a watannin baya an cafke Alkarya kam zargin karbar cin hanci.

Ko a satin da ya wuce sai da hukumar DSS ta cafke shugaban hukumar kare hakkin mai saye, Janar Idris Bello Dambazau, kan zargin yi wa tattalin arziki zagon kasa.