An cafke uwa tana kokarin sayar da jaririnta a Legas

Jama’ar gari sun gano shirin mutanen na siyar da jaririyar.

An cafke uwa tana kokarin sayar da jaririnta a Legas

‘Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wata uwa da wata mata, wadanda ake zargin su da yunkurin sayar da jaririyarta ’yar wata tara.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a ranar Asabar a wata sanarwa.

Hundeyin ya ce rundunar da dakile kokarin aikata wannan aika-aikar.

Ya ce an gano shirin cefanar da jaririyar ne a unguwar Oshodi, a lokacin da aka kama wani matashi mai shekara 25, wanda shi ne ya yi kokarin nemo masu sayen jaririn.

“Jama’ar yankin ne suka gano yadda jaririn ke kuka kuma an gaza samun wanda zai kula da shi.

“An kusa kashe wadanda ake zargin bayan da aka gano shirinsu.

“Bincike ya nuna cewa mahaifiyar jaririn mai suna Maria Ahmadu, mai shekara 26, ta bai wa matashin jaririn don ya sayar mata. Hakan ya sa aka kama matashin da uwar,” in ji shi.

Hundeyin ya ce an mika wadanda ake zargin da jaririn zuwa sashen kula da jinsi na rundunar domin ci gaba da bincike sannan za a gurfanar da su gaban kuliya.