An cafke wata mata kan sayan jaririyar wata 3 a Ekiti

Matar ta musanta zargin sayan jaririyar.

An cafke wata mata kan sayan jaririyar wata 3 a Ekiti

Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP), ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen sayar da wata jaririya a kan Naira miliyan biyu.

Shugabar NAPTIP a Ekiti, Mista Oladimeji Samson, ya ce jami’an tare da hadin gwiwar wasu a Jihar Ekiti ne, suka cafke wadanda ake zargin.

A cewarsa, daya daga cikin wadanda ake zargin, ta sayar da jaririyar ga wata, kan Naira miliyan biyu.

Wacce ake zargin da sayen jaririyar, ta musanta zargin, inda ta ce ta ita ta haifi jaririyar kuma bayar da ita ne domin kula da ita.

Ta ce, “Sun ce na sayi jaririya; wanda ba gaskiya ba ne. An kama ni a Ekiti. Ko da yake, ban haihu a asibiti ba amma a gidan matar da ake zargin na sayar da jaririyar na haihu. Kullum muna siyan magani a wajenta; a wata uku mun kashe Naira 100,000, sannan Naira 300,000 a wata tara.

“Bayan na haihu, maganin ya koma Naira 20,000. Na biya ta hanyar canja wuri. Ina biyan kudin ne ta hanyar banki. ‘Yar uwata ta rako ni Owo domin haihuwa.”

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa