An cashe a bikin Dini da Amina

An cashe a bikin shahararren jarumin fina-finan Hausa Zaharaddeen Sani da aka fi sani da Dini da amaryarsa Amina Hussaini.An daura auren a masallacin Juma’a na Aminuddin da ke daura da Ni’ima Hotel a Unguwar Badawa a Kano bayan sallar juma’a a kan sadaki Naira dubu 50 a ranar Juma’ar makon jiya.Bayan an daura auren […]

An cashe a bikin Dini da Amina

Ango Dini da amaryarsa Amina. A sama daga dama Wakilin jaridar Rariya Aliyu Ahmad neAn cashe a bikin shahararren jarumin fina-finan Hausa Zaharaddeen Sani da aka fi sani da Dini da amaryarsa Amina Hussaini.
An daura auren a masallacin Juma’a na Aminuddin da ke daura da Ni’ima Hotel a Unguwar Badawa a Kano bayan sallar juma’a a kan sadaki Naira dubu 50 a ranar Juma’ar makon jiya.
Bayan an daura auren ne da yamma aka buga wasan kwallon kafa tsakanin ’yan fim din Kaduna da kuma na Kano a filin kwallon kafa na Ranchers Bees da ke garin Kaduna, inda ‘yan wasan fim na Kaduna suka yi nasara da ci 2 da 0.
Wadanda suka buga a bangaren Kaduna akwai ango Dini da Umar M. Sharif da Kabir A. Zango da sauransu. Daga bangaren Kano kuma akwai Umar Kanu da Ali Jita da Usman Mu’azu da Yunusa Mu’azu da sauransu. Kabir da Umar M. Sharif ne suka ci kwallayen.
Washe gari Asabar aka gudanar da walima a dakin taro na Gamji da ke Kaduna da misalin karfe hudu na yamma.
‘Yan fim da yawa musamman mata ba su halarci bikin ba, haka ‘yan fim da yawa ba su halarci daurin auren a Kano ba.