An ceto daliban jami’a da aka yi garkuwa da su a Katsina
’Yan sana sun ceto daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma a Jihar Katisa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
’Yan sana sun ceto daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma a Jihar Katisa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Rundunar ’yan sandan jihar ta sanar a ranar Juma’a cewa jami’anta sun ceto daliban ne tare da wani dattijo mai kimanin shekaru 55 daga hannun ’yan ta’addar.
- Gawa ta yi layar zana ana shirin jana’izarta
- Akasarin wadanda za a nada ministoci na da hannu a matsalolin Najeriya — Masani
A ranar Alhamis ne ’yan ta’adda suka kai hari unguyar Bayan Radio da ke Dutsinma suka yi garkuwa da mutanen su uku.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce bayan harin ne rundunar ta kaddamar da bincike ta bi sahun maharan cikin daji inda a karshe ta yi nasarar ceto su, aka kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.