An ceto dukkanin fasinjojin da aka sace a Binuwai — Gwamna
Gwamnan ya tabbatar da ceto fasinjojin yayin ganawa da manema labarai.
Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce an ceto dukkanin fasinjojin da aka sace a wata bas da aka kai wa hari.
Gwamnan, ya tabbatar da ceto mutanen yayin da yake magana da manema labarai, amma bai bayyana ainihin adadin waɗanda aka sace ba.
- Ana ƙoƙarin shirya min sabuwar maƙarƙashiya — El-Rufai
- Gobara ta kone gidaje 1,000 a unguwar takalawa a Malaysia
Tun da farko, ’yan sanda sun ce mutane 14 aka sace, yayin da gwamnan ya ce mutane 15 ne.
’Yan sanda kuma sun ce an kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a harin.
Wannan lamarin ya nuna yadda hare-hare da sace-sacen mutane ke ƙara ƙamari a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar.
Yawanci ƙungiyoyin ’yan bindiga ne ke kai hare-haren domin neman kuɗin fansa.
Jihar Binuwai kuma na daga cikin wuraren da ake yawan samun rikici tsakanin makiyaya da manoma.