An ceto jaririn da aka sayar mako daya da haihuwarsa

Gwamnatin Jihar Edo ta ceto wani jariri dan kimanin sati daya da haihuwa daga hannun masu cinikin jarirai a tsakanin jihar da kuma Anambra. Kwamishinar Shari’a ta Jihar kuma shugabar kwamitin yaki da safarar mutane a Jihar, Farfesa Yinka Omorogbe ta ce dillalan sun sayar da jaririn a kan N300,000, kuma an gurfanar da su […]

An ceto jaririn da aka sayar mako daya da haihuwarsa

Gwamnatin Jihar Edo ta ceto wani jariri dan kimanin sati daya da haihuwa daga hannun masu cinikin jarirai a tsakanin jihar da kuma Anambra.

Kwamishinar Shari’a ta Jihar kuma shugabar kwamitin yaki da safarar mutane a Jihar, Farfesa Yinka Omorogbe ta ce dillalan sun sayar da jaririn a kan N300,000, kuma an gurfanar da su a kotu domin su girbi abun da suka shuka.

“A ranar 5 ga Agusta, sashen bincike na kwamitinmu ya gano wani gidan da ake amfani da shi wajen cinikin jarirai a jihohin Edo, Anambra da wasu sassan kasar nan.

“Bayan mun kama daya daga cikin dillalan mun titsiye ta, sai ta fada mana sunan wata mata a Jihar Anambra, inda a nan ne gidan cinikin jariran yake”, inji ta.

Ta kuma ce bayan da suka kama matar ta Anambra sai ta shaida wa jami’ansu cewa jaririn da mahaifiyarsa na zaune ne a wani asibiti.

Daga bisani matar ta jagoranci ‘yan kwamitin zuwa asibitin da matar ta haifi jaririn tare da kama unguwarzomar da ke karbar haihuwa a wurin.

Ta ce kwamitin ya gano wata budurwa da ta haihu ranar 28 ga watan Yuli da aka sayar da jaririn nata bisa alkawarin za a ba ta Naira 300,000 a matsayin kasonta.

“Mun kuma samu matar da wata budurwar wacce ke dauke da juna biyu kuma ta kusa haihuwa kuma ta kasa cikakken bayanin makasudin zamanta a gidan”, inji shugabar kwamitin.

An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Legas

Hajjin 2025: An sanar da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyata

Boko Haram sun kashe manoma 40, wasu sun ɓace a Borno

Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji