An ceto karin dalibar Chibok da wasu mutane 96 a
Dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki a sansanin ’yan Boko Haram da ke dajin Sambisa, inda suka ceto mata da kananan yara 99 ciki har da daya daga cikin Daliban Makarantar Chibok, Ihyi Abudu da ’ya’yanta biyu. Hakan na zuwa ne yayin da sojojin ke ci gaba da kakkabe ’yan ta’addan a dajin Sambisa, Timbuktu […]
Dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki a sansanin ’yan Boko Haram da ke dajin Sambisa, inda suka ceto mata da kananan yara 99 ciki har da daya daga cikin Daliban Makarantar Chibok, Ihyi Abudu da ’ya’yanta biyu.
Hakan na zuwa ne yayin da sojojin ke ci gaba da kakkabe ’yan ta’addan a dajin Sambisa, Timbuktu da sauran sassan yankin Arewa maso Gabas.
Wasu majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa Dalibar Chibok da aka ceto wacce ke lamba 67 a jerin daliban da aka sace, ta tsere ne daga maboyar ’yan ta’addan na Parisu.
Sojoji sun kubutar da ita ne a wani samame da aka kai a yankin Bararam a Dajin Sambisa.
Majiyar ta kara da cewa a lokacin da suke shiga sansanin ’yan ta’addan, sojojin sun ceto wasu mutane 99 da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Mutanen da aka ceto sun hada da mata 41 da kananan yara 57 da kuma dalibar Chibok din da ’ya’yanta biyu.
Nan take suka mika wuya ga dakarun sojan cikin farin ciki.
Ya bayyana cewa, bayan nasarar da rundunar ta samu na kubutar da su, jami’an kiwon lafiya na sojojin Najeriya sun sun tantance su inda aka gano yawancinsu na fama da yunwa sakamakon rashin abinci mai gina jiki, rashin ruwa, da kuma cututtuka
A cewar majiyar, a halin yanzu ’yan Boko Haram sama da 161,000 da iyalansu suka mika wuya ga sojojin a yayin farmaki daban-daban.
Ya kara da cewa aikin ceton na nuni ne da irin jajircewar da sojojin Najeriya ke yi na kare fararen hula da kuma kare hakkin bil Adama.
Halin da ’yan matan Chibok suka fuskanta ya dauki hankulan duniya, kuma ceto su ya kasance wani abin fatan alheri ga al’umma da al’ummar da suka sha wahala sosai a hannun ta’addancin Boko Haram tsawon shekaru.