An ceto karin Dalibar Chibok da ’ya’ya da juna-biyu a Borno

An gano cewa Dalibar Chibok din da aka ceto tana dauke da juna biyu, kuma aurenta biyu da ’yan Boko Haram

An ceto karin Dalibar Chibok da ’ya’ya da juna-biyu a Borno

A wani gagarumin cigaba da aka samu, dakarun Operation Hadin Kai sun yi nasarar ceto wata ’yar Makarantar Chibok mai suna Ihyi Abdul da ’ya’yanta biyu a garin Bama na Jihar Borno.

Wannan dai ya kawo adadin ’Yan Matan Chibok da aka ceto zuwa 19.

An ceto Ihyi Abdul, mai shekaru 27, a ranar 23 ga watan Yuni, 2024, tare da ’ya’yanta guda biyu ne a wani samame da sojojin suka kai a dajin Sambisa.

An bayyana ta a matsayin mai lamba 67 a cikin jerin ’Yan Matan Makarantar Chibok da Gwamnatin Tarayya ta wallafa a shekarar 2014.

Babban kwamandan runduna ta 7 ta Sojan Najeriya, Birgediya-Janar AGL Haruna, ya ce, Ihyi Abdul ta yi aure da wani dan ta’adda mai suna Abu Darda a shekarar 2014, wanda daga bisani ya koma kasar Senegal.

Bayan an kashe Abu Darda, ta sake yin aure da wani dan ta’adda, Bana a Garin Mustapha, Njimiya, cikin dajin Sambisa.

Ya ce ’yar Chibok da aka ceto tare da ’ya’yanta an musu cikakken binciken duba lafiyarsu tare da kula da su a wani asibitin sojoji.

Sannan ya ce halin yanzu tana da cikin wata uku kuma tana samun kulawar da ta dace.

“Tana da shekara 27, ’yar kablilar Kibaku kuma Musulma ce daga kauyen Kubur-Mbula a Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.

“Tunin dai aka  mika Ihyi Abdu da ’ya’yanta 2, Khadija da Anas ga wakilan Gwamnatin jihar Borno,” in ji Janar Haruna.

Kwamandan Rundunar Operation Hadun Kai, Manjo-Janar Wahidu Shaibu, ne ya sanar da ceto ’Yar Makarantar Chibok din da ’ya’yanta a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke barikin Sojoji na Maimamalari da ke Maiduguri.

Manjo-Janar Shaibu ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu, inda ya bayyana cewa ceton wata shaida ce ta jajircewarsu na kawo karshen tashe-tashen hankula da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Kwamishiniyar Al’amuran Mata da Cigaban Jama’a ta Jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, wacce Daraktar Jin Dadin Jama’a, Hajiya Aisha Shettima ta wakilta, ta karbi bakuncin Ihyi Abdul da ’ya’yanta a madadin gwamnatin jihar.

Kwamishinar ta gode wa sojojin bisa kokarin da suka yi, ta kuma ba da tabbacin cewa dalibar da ’ya’yanta za su samu kulawar da ta dace da kuma tallafi a cibiyar farfado da su da ke Biulumkutu.