An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara
An kuma ƙwato ɗaruruwan shanun da ’yan bindiga suka kwashe a wasu hare-hare daban-daban da suka faru a ƙananan hukumomin Gummi da Talata Mafara da Gusau.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce, ta ceto wani ma’aikacin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da aka yi garkuwa da shi, tare da wasu mutanen da aka sace.
Sannan ta ƙwato ɗaruruwan shanun da ’yan bindiga suka kwashe a wasu hare-hare daban-daban da suka faru a ƙananan hukumomin Gummi da Talata Mafara da Gusau.
- Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama
- Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya ce ’yan bindigar sun kai hari wasu ƙauyuka a Talata Mafara inda suka kwashe shanu masu yawa tare da harbin wata mata da ke ci gaba da jinya a asibiti.
Ya ce, daga baya maharan sun sace wani ma’aikacin INEC, Aliyu Mohammed wanda ke aikin jigilar takardun jarrabawar NECO daga Gummi zuwa Sakkwato.
Sai dai jami’an tsaro sun gano motarsa da takardun jarabawar tare da mayar da takardun ga hukumomin da abin ya shafa.
A cewarsa, bayan samun bayanan sirri, jami’an ’yan sanda tare da sojoji sun bi sahun ’yan bindigar zuwa dajin Gando, inda suka yi musayar wuta da su.
Ya ce, hakan ya tilasta wa maharan tserewa da raunukan harbin bindiga, yayin da aka ceto ma’aikacin INEC da wani mutum da aka yi garkuwa da shi ba tare da sun ji rauni ba, tare da ƙwato ɗaruruwan shanun da aka sace.
Rundunar ta ce, a wani samame daban da aka kai a yankin Kwanar Ganuwa da ke Ƙaramar Hukumar Gusau, an kuma ceto duk mutanen da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, bayan jami’an tsaro sun fatattaki maharan zuwa cikin daji.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A.M. Bello ya yaba wa jami’an tsaron, tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da ba wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da ’yan bindiga.