An ceto mai gari da wasu 3 da aka yi garkuwa da su

’Yan sanda sun yi nasarar ceto mai garin da sauran mutanen da aka sace.

An ceto mai gari da wasu 3 da aka yi garkuwa da su

’Yan sanda a Jihar Ebonyi sun ceto mutum hudu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Oshiagu Amia-Ngbo, a Karamar Hukumar Ohaukwu.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da ceto mutanen a ranar Juma’a a garin Abakaliki.

“Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen, amma mun samu nasarar ceto su.

“Ina so na yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin mutane da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri.

“Abun mamaki shi ne yi garkuwa da mai gari da wasu mutum uku, tun karfe 2 na dare amma babu wanda zai sanar da ’yan sanda.

“Amma labari ma fi dadi shi ne am ceto su, kuma na tabbatar za su sanar da ’yan sandan yankin abin da ya faru,”a cewar Odah.

Kazalika, ta ce tilas ne sai mutanen sun taimaka matukar ana so a yaki ta’addanci a jihar.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna