An ceto mata 2 bayan kashe ’yan ta’adda 6 a Borno da Yobe
Sojojin sun kuma kama wasu da ake zargi da haɗa kai da ’yan ta’adda tare da gano bama-bamai da aka dasa a kan hanyoyi.
Matan da aka ceto
Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda shida tare da ceto mata biyu da aka sace a wasu hare-hare da suka kai a jihohin Borno da Yobe.
Rundunar ta ce ta kuma ƙwato makamai da abubuwan fashewa a hare-haren da aka gudanar ƙarƙashin Operation Desert Sanity domin murƙushe ayyukan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.
- ’Yan ta’adda sun sace mutane a Fadar Sarki a Kwara
- An ƙara N5000 a kudin mota daga Kano zuwa Zamfara
Kakakin rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya bayyana cewa sojojin sun samu nasarorin ne a wurare daban-daban, ciki har da yankin Mazga da ke kan hanyar Buni/Yadi zuwa Biu, inda aka gano makamai da abubuwan fashewa da mayaƙan suka bari bayan sun tsere.
Ya ce sojojin sun kuma kama wasu da ake zargi da haɗa kai da ’yan ta’adda tare da gano bama-bamai da aka dasa a kan hanyoyi.
A cewarsa, dakarun tare da goyon bayan ƙungiyar CJTF sun kai samame yankunan Valle, Ashigashiya da Gakara, inda suka yi artabu da mayaƙan Boko Haram/ISWAP.

“Mun kashe ’yan ta’adda biyu a yayin gumurzu, yayin da wasu suka tsere zuwa yankin Ngoshe,” in ji shi.