An ceto matan ’yan sanda da aka yi garkuwa da su a Ribas
Jami’an sashin binciken manyan laifuffuka daga ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya sun ceto matan ’yan sanda biyu da sauran mutum takwas da masu garkuwa da mutane suka sace a kan Titin Fatakwal zuwa Owerri a kwanakin baya. Mutanen da aka sacen suna komowa gida ne daga Anaca, Jihar Anambra. Kwamandan jami’an, Benneth Igwe, […]
Jami’an sashin binciken manyan laifuffuka daga ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya sun ceto matan ’yan sanda biyu da sauran mutum takwas da masu garkuwa da mutane suka sace a kan Titin Fatakwal zuwa Owerri a kwanakin baya.
Mutanen da aka sacen suna komowa gida ne daga Anaca, Jihar Anambra. Kwamandan jami’an, Benneth Igwe, ya bayyana wa ’yan jarida cewa sun kwashe kwana uku a cikin daji suna bincike, kafin su yi nasarar ceto mutanen. Ya ce tunda farko sai da suka kai mutanen da suka ceto zuwa Kwalejin Sojan Ruwa da ke Ubima, inda aka duba lafiyarsu, sannan aka wuce da su zuwa garin Aluu, aka sada su da iyalansu.
Wadansu daga cikin mutanen da aka yi garkuwar da su, sun bayyana cewa sun sha bakar wahala a hannun barayin, wadanda suka kwace abubuwan da suke hannunsu, sannan suka yi musu barazana da tsoratarwa, suka ce za su kashe su muddin ba su kirawo ’yan uwansu ba domin su biya kudin fansa.
Direban motar da aka kama mutanen a ciki, mai suna Uzuoma Iwuala ya bayyana cewa wadansu daga cikinsu sai da suka biya kudin fansa kafin su samu kansu. Daya daga cikinsu ma ya ce sai da suka kwace musu katin cirar kudi a banki (ATM), suka ciri kudade masu yawa daga asusun ajiyarsu na banki.