An ceto matar marigayi Janar Rabe

Sojoji sun ceto Amina Abubakar bayan ɓarin wuta da ’yan bindiga amma sun harbi matar kafin su sake ta su tsere cikin daji.

An ceto matar marigayi Janar Rabe

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ceto Hajiya Amina Abubakar, uwargidan tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, marigayi Manjo-Janar Rabe Abubakar.

Bayanai sun ce dakarun sojin Najeriya da ke ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YANMA ne suka ceto matar tsohon sojan bayan wani samame da suka kai kan ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Matazu da ke Jihar Katsina.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne a ƙarƙashin rundunar Operation CLEAN SWEEP III, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka biyo bayan harin da aka kai wa iyalan tsohon babban hafsan sojin.

Zagazola Makama, ƙwararren mai fashin-baƙi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, ya ruwaito majiyar sojin na cewa sun yi artabu da ’yan bindigar ne a ƙauyen Tunga yayin wani aikin bincike da ceto, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan harbin matar sannan suka tsere sakamakon ruwan wuta da sojojin suka yi musu.

“Mun yi nasarar ceto Misis Abubakar. Ta samu raunin harbin bindiga kuma tana zubar da jini. Amma tuni muka ba ta agajin gaggawa kafin a garzaya da ita cibiyar lafiya domin ci gaba da kula da lafiyarta,” in ji majiyar.

Sojojin sun ce ana ci gaba da sintirin neman maharan da suka tsere, tare da ƙara ƙaimi wajen farautar waɗanda ake zargi da hannu a harin da kuma sace-sacen mutane da suka wakana a yankin.

Sun kuma tabbatar da cewa aikin kawar da maɓoyar ’yan bindiga a ƙarƙashin rundunar Operation CLEAN SWEEP III zai ci gaba da gudana har sai an tarwatsa dukkan sansanoninsu.

Majiyoyin tsaro sun jaddada cewa rundunar sojin Najeriya ta yi tsayin-daka wajen tabbatar da kamo masu hannu a harin domin su fuskanci hukuncin doka.

Janar Rabe ya mutu a hannun ’yan bindiga

A ranar Asabar da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (Ritaya) a hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa shi.

Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu, ya bayyana cewa Manjo-Janar Rabe Abubakar ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga, duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi na tabbatar da an kuɓutar da shi.

Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini.

Gwamnatin ta nuna matuƙar alhini kan lamarin, tana mai cewa sace marigayin da kuma rasuwarsa daga bisani babban rashi ne ba ga iyalansa da Jihar Katsina kaɗai ba, har ma ga Nijeriya baki ɗaya.