An ceto matashin da ya yi kwana 49 yana watan-gaririya a teku

Wani matashi dan kasar Indonisiya wanda ke kula da wata bukka ta musamman ta kamun kifi da ake sanyawa a teku ya rayu tsawon kwana 49 yana watangarirya a cikin teku ta hanyar dafa kifin da yake kamawa yana ci. Aldi Nobel Adilang yana cikin bukkar ne a wani wuri mai nisan kilomita 125 daga […]

An ceto matashin da ya yi kwana 49 yana watan-gaririya a teku

Wani matashi dan kasar Indonisiya wanda ke kula da wata bukka ta musamman ta kamun kifi da ake sanyawa a teku ya rayu tsawon kwana 49 yana watangarirya a cikin teku ta hanyar dafa kifin da yake kamawa yana ci.

Aldi Nobel Adilang yana cikin bukkar ne a wani wuri mai nisan kilomita 125 daga bakin gabar tekun Indonisiya a tsakiyar watan Yuli lokacin da wata iska mai karfi ta kada bukkar matashin mai shekara 18 zuwa can cikin teku ya yi ta watan-gaririya.

Hakan ya yi ta nausawa cikin tekun har nisan dubban kilomita zuwa kusa da Tsibirin Guam na tekun Pacific wanda ke karkashin Amurka, har sai da wani jirgin ruwa na kasar Panama ya ceto shi, inji BBC.

Matashin wanda dan tsibirin Sulawesi ne na kasar Indonisiya, yana aiki ne a wata bukka ta musamman ta kamun kifi da ake sanyawa a cikin teku tana yawo, ba tare da wani inji ko abin tukin kwalekwale ba.

Aikinsa shi ne ya kunna fitilun bukkar, wadanda aka tsara su yadda za su jawo hankalin kifi, wato kamar tarko, kamar yadda jaridar Jakarta Post ta ruwaito.

Tarkon wanda aka tsara shi kamar bukka yana yawo ne a kan teku amma kuma ta can kasa an daddaure shi da igiya a ciyayin karkashin teku.

Kowa ne mako akwai wani daga kamfanin da matashin yake aiki da yake zuwa can cikin tekun ya kai masa abinci da ruwan sha da kananzir, sannan ya tafi da kifin da ya kama.

Tun a ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata ne wata iska mai karfin gaske ta yi gaba da bukkar  Mista Adilang, ya yi ta yawo a kan teku. Kuma kasancewar kayan abincinsa ba su da yawa, sai ya rika kama kifi yana gasawa da katakon da aka yi dangar bukkar.

Ya ce hankalinsa ya tashi ya ji tsoro har ya rika kuka  lokacin da bukkar ke yawo da shi a teku. Kamar yadda Fajar Fidaus wani jami’in diflomasiyya na Indonisiya a birnin Osak na Japan, ya gaya wa jaridar Jakarta Post.

Mahaifiyarsa ta gaya wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP yadda ta samu labarin bacewar dan nata. “Mai gidansa ya gaya wa mijina cewa ya bata,’’ inji Net kahiking. “Shi ke nan muka bar wa Allah al’amarin muka rika addu’a.’’

A ranar 31 ga Agusta, Mista Adilang ya aika da sakon oba-oba na neman agajin gaggawa lokacin da ya ga jirgin ruwan Mb Arpeggio a kusa.

Daga nan ne mutanen jirgin ruwan na Panama suka ceto shi daga yankin tekun na Tsibirin Guam.

Matukin jirgin ruwan ya tuntubi jami’an tsaron gabar tekun Guam wadanda su kuma suka ba shi dama ya kai shi Japan, inda jirgin zai je, kamar yadda wata sanarwa daga karamin ofishin jakadancin Indonisiya a Osaka ta bayyana.

A ranar 6 ga Satumba, Mista Adilang ya isa Japan daga nan bayan kwana biyu aka mayar da shi Indonisiya inda aka hada shi da iyayensa. Kuma an ce yana cikin koshin lafiya yanzu.

“Yanzu ya komo gida kuma a ranar 30 ga watan Satumba zai cika shekara 19 – za mu shirya masa liyafa a ranar,’’ in ji mahaifiyarsa.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana