An ceto mutane 386 bayan shekaru 10 a hannun Boko Haram

Sojoji sun fararen hula 386 daga Dajin Sambisa, bayan Boko Haram ta sace su kimanin shekaru goma da suka gabata.

An ceto mutane 386 bayan shekaru 10 a hannun Boko Haram

Sojoji sun ceto fararen hula 386, akasarinsu mata da kakanan yara, daga Dajin Sambisa, bayan Boko Haram ta sace su kimanin shekaru goma da suka gabata.

Mai rikon mukamin Babban Kwamandan Birget Din Sojin Kasa Na 7, Birgedia AGL Haruna, ne ya bayyana haka ranar Lahadin yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dajin da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno sakamakon nasarar kammala wani aiki na kwanaki 10 da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111”.

A cewarsa, an kai farmakin ne da nufin kawar da duk wani burbushin Boko Haram da sauran ’yan ta’adda da ke dajin gami da bayar da dama ga masu son mika wuya su yi hakan.

Janar Haruna ya bayyana fatansa na cewa karin ’yan ta’adda za su mika wuya, inda ya bayyana yadda suke ci gaba da mika wuya ga sojoji.

“Kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ’yan ta’adda a Sambisa, tare da bai wa masu son mika kansu damar yin hakan.

“Da wannan aiki, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.

“Mun kuma ceto wasu fararen hula guda 386 a ranar 17 ga Mayu, 2024; kuma na tabbata adadin zai karu,” inji Haruna.

Janar Haruna ya yaba wa sojojin bisa kwazon da suka nuna, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Wasu daga cikin mutanen da aka ceto sun yi magana game da mummunan halin da suka shiga, bayan da suka shafe shekaru goma a hannun Boko Hara a Dajin.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume