An ceto mutum 10 bayan ruftawar gini hawa uku a Legas
Masu kashe gobara sun isa cikin ’yan mintuna kaɗan kuma suka fara ayyukan ceto a daidai wurin da ginin ya rushe, wanda aka ruwaito cewa akwai mazauna da dama a cikinsa a lokacin da lamarin ya faru.
An ceto mutane 10 da rai a ranar Alhamis bayan ruftawar wani gini mai hawa uku a yankin Satellite Town da ke Jihar Legas.
Wannan lamari ya janyo gagarumin binciken gaggawa daga jami’an tsaro da na ceto, inda har yanzu ake ci gaba da bincike don fito da waɗanda ka iya kasancewa maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.
- An dakatar da shugaban jam’iyyar APC da Kwamishina a Kebbi
- Gwamnatin Gombe ta buɗe sabuwar kasuwar kayan lambu mai shaguna 160
Lamarin ya faru ne a kan titin Old Ojo Road, kusa da tashar mota ta Alakija, daidai babbar hanyar mota ta Legas zuwa Badagry.
Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas ta bayyana cewa, ta sami kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:37 na safe, kuma nan da nan ta tura jami’an agaji daga Tashar Kashe Gobara ta Ijegun-Egba zuwa wurin da abin ya faru.
Masu kashe gobara sun isa cikin ’yan mintuna kaɗan kuma suka fara ayyukan ceto a daidai wurin da ginin ya rushe, wanda aka ruwaito cewa akwai mazauna da dama a cikinsa a lokacin da lamarin ya faru.
Babbar Jami’ar Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas, Margaret Adeseye ta tabbatar da cewa an fito da mutane 10 da rai daga cikin baraguzan ginin.
Ta ce, “Mutanen da aka ceto sun sami raunuka daban-daban kuma an miƙa su ga ma’aikatan lafiya domin yi musu magani.”
Ta ƙara da cewa, har yanzu ana ci gaba da ayyukan ceto yayin da ma’aikatan gaggawa ke ci gaba da bincika baraguzan ginin domin gano sauran mazauna da ka iya kasancewa a maƙale.
Aikin ceton ya sami goyon baya daga hukumomin gaggawa da na tsaro daban-daban, ciki har da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, Hukumar Tsaron Unguwanni ta Legas (LNSC), da kuma ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya.