An ceto mutum 24 a hatsarin jirgin ruwa a Kogi
Gwamnatin ta kuma miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwan.
Gwamnatin Jihar Kogi, ta tabbatar da ceto mutum 24 bayan jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 200 ya kife a Kogin Neja ranar Juma’a.
Waɗanda aka ceto suna asibiti ake ba su kulawa ƙarƙashin kulawar likitoci.
- Mutane da yawa ba su fahimci yadda ƙudirin dokar haraji yake ba – Barau
- Gwamnatin Kano ta mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama tsohon sunanta
Gwamnan Jihar, Ahmed Usman Ododo, ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA), da ta tallafa wa iyalan mutanen da hatsarin ya shafa.
Sannan ya buƙaci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, ta tabbatar da cewa an bai wa waɗanda suka kuɓuta kulawar da ta dace.
“Gwamnatin Jihar Kogi tana cike da alhini kan wannan mummunan lamari,” in ji Kinsley Fanwo, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar.
“Mun tabbatar da cewa an ceto mutum 24, kuma suna samun kulawa. Har yanzu aikin ceto yana gudana, kuma muna kira ga masu aiki a ruwa su bi ƙa’idojin tsaro don kauce wa irin wannan hatsari a gaba.”
Gwamnatin ta kuma yaba wa ƙoƙarin ƙungiyoyin da suka taimaka wajen aikin ceto, ciki har da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA) da River Marshals.
Har ila yau, an gano gawar mutum takwas, sannan gwamnatin ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Hatsarin ya faru ne yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga Kupa Ebe a Jihar Kogi zuwa Kasuwar Katcha da ke Jihar Neja.