An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Gwamnatin jihar ta nemi haɗin ‘yan Najeriya wajen kawo ƙarshen ayyukan mahara.

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya miƙa wa Gwamnatin Jihar Kaduna, mutum 58 da aka ceto daga hannun ’yan bindiga.

An kuɓutar da mutanen ne ta hanyar haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ba a biya kuɗin fansa don kuɓutar da su ba.

Ya ce an yi amfani da dabarun soja da tattaunawa cikin lumana, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Najeriya gaba ɗaya yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma nasarar ayyukansu.

Waɗanda aka kuɓutar; maza 35 da mata 23, an sace su ne a wasu ƙauyuka na Jihar Katsina.

An tilasta musu yin doguwar tafiya a cikin dazuzzuka kafin a ceto su.

An kuɓutar da su ne yayin wani samame da sojoji suka kai a ranar 14 ga watan Nuwamba.

Bayan an ceto su, an duba lafiyarsu, kafin miƙa su ga gwamnatin jihar.

Mutane shida da aka kwantar domin yin jinya sun warke, insa aka haɗa su da sauran ’yan uwansu.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kaduna, Sani Limankila, ya gode wa hukumomin tsaro, sannan ya yi kira ga ’yan Najeriya su haɗa kai domin kawo ƙarshen sace-sacen mutane.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta