An ceto mutumin da ’yan bindiga suka sace a Abuja

Maharan sun sace mutumin ne a kan hanyar zuwa titin jirgin saman Abuja.

An ceto mutumin da ’yan bindiga suka sace a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ceto Suleiman Sabo da ‘yan bindiga suka sace a kan hanyar zuwa titin jirgin saman Abuja.

An ruwaito cewar Sabo na kan hanyarsa ta komawa gida tare da matarsa lokacin da ‘yan bindigar suka tare motarsa.

Mutumin na tsaka da tuka motarsa kirar Lexus Jeep mai lamba ABC 769 TP, lokacin da lamarin ya faru.

Maharan sun biyo bayansa a wata mota kirar Golf, inda suka bude masa wuta tare da fasa tayoyin motarsa.

Sai dai Kwamishinan ’yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna Garba, ya bayyana cewar sun yi nasarar ceto mutumin a ranar Lahadi.

Kwamishinan, ya ce jami’an ’yan sandan ofishin Iddo da ke kauyen Sauka ne suka ceto mutumin.

Kazalika, ya ce an cafke wani dan asalin Jihar Kogi a yayin ceto mutumin, inda suka kwato bindiga da harsashi 10 a hannunsa.

A cewarsa, wanda aka ceto ya samu raunuka, amma a halin yanzu yana asibiti, inda likitoci ke kula da lafiyarsa.

Kwamishinan, ya tabbatar da kudurin rundunar na tabbatar da tsaro da birnin tarayya da kewaye.

Sannan ya bukaci mazauna Abuja da su kira wadannan lambobi da zarar sun ga wani abu da ke bukatar dauki; 08032003913, 08061581938, 07057337653, 08028940883 da kuma 09022222352.

Har wa yau, rundunar ta ceto wasu mazauna Abuja da aka sace a farkon watan Janairu, 2024.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja