An ceto sauran daliban Jami’ar Gusau da ’yan NYSC da ke hannun masu garkuwa
’Yan bindiga sun sako ragowar dalibai da ma’aikatan Jami’ar Tarayya da ke Gusau da suka sace a watan Satumbar 2023 da kuma masu yi wa kasa hidimia (NYSC ) da ke hannunsu
’Yan bindiga sun sako ragowar dalibai da ma’aikatan Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara, wadanda aka yi garkuwa da su a watanni bakwai da suka gabata.
A ranar 22 ga Satumbar 2023 ne mahara suka kutsa dakunan kwanan daliban da ke unguwar Sabon-Gida a Karamar Hukumar Bungudu a jihar Zamfara, suka sace dalibai sama da 20, yawancinsu mata.
Bayan kokarin da hukumomin jami’ar da dangin daliban suka yi, ta’addan sun sako wasu daga cikinsu bayan watanni, amma suka ci gaba da rike ragowar 23.
Sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaro sun ceto sauran daliban a ranar Lahadi.
- Mutum 3 sun rasu an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe
- NAJERIYA A YAU: Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi
Wata majiya da ke da masaniyar lamarin kai tsaye ta ce “An saki jimillar mutane 23 ne a Kuncin Kalgo da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara kuma aka mika su ga jami’an gwamnati a ranar Lahadin.”
Aminiya ta ga hotunan wasu da aka yi garkuwa da su a cikin motocin bas.
An ceto ’yan NYSC da aka sace
Majiyar ta kara da cewa an kubutar da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka sace a Jihar Sakkwato.
Zamfara na daga cikin jihohin da matsalar ’yan bindiga ta fi shafa a yakin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Yayin ganawarsa da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock a watan jiya, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce ’yan ta’adda sun yi wa jiharsa kawanya.
“Ina jin a matsayina na gwamna, ya kamata in sanar da shugaban kasa hare-haren da aka kai jihar Zamfra, kuma ya ji dadin tattaunawar da muka yi, kuma muna neman karin sojoji da kayan aikin da za su yi aiki yadda ya kamata da kuma kula da su. yanayin tsaro.
“Zamfara ta zama cibiyar ’yan bindiga, kuma idan ba a yi wani abu a jihar Zamfara ba, ba na jin za mu iya magance matsalar a Arewacin Najeriya baki daya.
“Mafi yawan wadanda ake sacewa a jihar Kaduna, Zamfara ake kai su, wanda bai dace da mu ba, don haka muna yin duk abin da za mu iya domin kawo karshen lamarin, kuma wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa na zo ganin shugaban kasa.
“Don haka ne na zo nan na sanar da shugaban kasa kuma ina da tabbacin cewa za a yi wani abu mai tsauri don shawo kan lamarin da wuri,” in ji gwamnan a wancan lokacin.