An ceto shugaban kamfanin LG daga hannun ’yan bindiga

An yi garkuwa da ’yan kasar Lebanon ukun tare da ma’aikatansu ’yan Najeriya ne hanyarsu zuwa gidansu da ke yankin Banana Island a cikin jirgin ruwa

An ceto shugaban kamfanin LG daga hannun ’yan bindiga

Jami’an tsaron hadin gwiwa sun ceto Manajan Daraktan kamfanin kayan laturoni na LG Hisense a Najeriya, Mohammed Foani, tare da ’yan uwansa biyu daga hannun masu garkuwa da mutane.

Sojojin ruwa da ’yan sandan tsaron teku sun ceto Mohammed Foani da ’yan uwan nasa wadanda dukkansu ’yan kasar Lebanon ne tare da direbobin jirgin ruwansu ’yan Najeriya, a safiyar Talata.

Aminiya ta gano cewa an gano tare da ceto su ne a maboyar masu garkuwa da su ne da ke unguwar  Orugbo Iddo a tsakanin jihohin Legas da Ondo.

A ranar Juma’a ne masu garkuwa da mutane dauke da bindigogi suka yi awon gaba da su Mista Foani a lokacin da suke tafiya cikin jirgin ruwa daga yankin Apapa zuwa gidansu da ke Banana Island da ke Jihar Legas.

Ana zargin masu garkuwa da su sun yi awon gaba da ’yan kasar Lebanon din tare da ma’aikatansu ’yan Najeriya ne su a kan teku ne a kusa da Gadar Falomo da ke Legas a cikin wasu kannan jiragen ruwan zamani masu tsananin gudu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da ceto wadanda aka sacen ne gabanin wayewar garin ranar Talata a Orugbo Iddo.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara