An ceto tsoho mai shekara 70 daga hannun masu garkuwa da mutane

Jami’an tsaro sun ceto wani tsoho mai kimanin shekara 70 mai suna Alhaji Sale Namairiga daga hannun masu garkuwa da mutane suna neman fansar kudi.Tsohon wanda ya kwashe kwana 12 a hannun masu garkuwa da mutanen, ya nuna farin cikinsa a lokacin da Aminiya ta tattaunawa da shi jim kadan bayan da iyalansa suka zo […]

An ceto tsoho mai shekara 70 daga hannun masu garkuwa da mutane
An ceto tsoho mai shekara 70 daga hannun masu garkuwa da mutane

Jami’an tsaro sun ceto wani tsoho mai kimanin shekara 70 mai suna Alhaji Sale Namairiga daga hannun masu garkuwa da mutane suna neman fansar kudi.
Tsohon wanda ya kwashe kwana 12 a hannun masu garkuwa da mutanen, ya nuna farin cikinsa a lokacin da Aminiya ta tattaunawa da shi jim kadan bayan da iyalansa suka zo amsarsa a hannun ’yan sanda. Alhaji Sale Namairiga wanda yake zaune a kauyen Janda da ke karamar Hukumar danja a Jihar Katsina, Ya shaida wa wakilinmu cewa “A ranar Litinin kwana 12 da suka wuce da misalin karfe 10 na dare na ji karnuka suna haushi sai na fito sai na ga wasu mutum hudu sun nufo ni dauke da bindigogi suka kama ni suka ce mu koma daki. Da muka shiga daki suka ce in ba su kudi, na ce musu babu domin kudin da ke hannuna ba yawa haka na kwashe na ba su sai suka rubuta takarda suka aje suka ce a sa a waya a kira su,  suka kama ni suka daure min ido duk da na bayyana musu cewa ni ba mai kudi ba ne, domin shanun da na mallaka ma kwaya 20 ne haka suka tarkata suka dora ni a kan babur suka tafi da ni wani kungurmin daji suka aje ni sai dai in tashi in yi Sallah in sun kawo mini abinci in ci, har na kwashe wadannan kwanaki a wurinsu.”
Alhaji Sale Namairiga ya ce iyalanasa sun kira shi a wayarsu a lokacin ne wadanda suka sato shi suka ce sai an ba su Naira miliyan uku kafin su sake shi, alhali baki daya dabbobinsu ba za su kai Naira miliyan uku ba. Ya ce haka aka yi ta tuturniya har sai da safe da hantsi suna zaune sai suka ji motsi ta gabashinsu sai daya daga cikin barayin mutanen ya ce ana motsi don haka su gudu ana cikin haka sai muka fara jin harbin bindiga. “Ni dai nan na yi kwance domin ba ni da karfin da zan gudu, na dauka sojoji ne sai da muka zo aka ce min ai ’yan sanda ne,” inji dattijon.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da shiyya ta daya a Jihar kaduna A.C Muhammadu D. Shehu ya ce sun sami labarin sace tsohon tare da neman kudin fansa da aka sa wa ’yan uwansa Naira miliyan uku, “Don haka na yi damara na tanadi man fetur lita 200, ni da abokan aikina da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Lahadi muka kama hanya zuwa dajin Kidandan kuma da ke iyaka da UAC da dajin Turnuku da suke iyaka da Maidaro. Sai da muka share tsawon awa uku da rabi domin yawancin tafiyar da kafa muka yi saboda mota ba ta isa wurin, mun isa wurin da misalin karfe 9:00 na safe muka samu wata rugar Fulani cikin dokar daji nan muka yi ta artabu da maharan, mun samu nasarar ceto wannan tsoho da lafiyarsa, mun kuma kama daya daga cikin barayin mutanen, kuma mun kashe daya yayin artabun. Yanzu haka mun mika Alhaji Sale Namairiga ga ’yan uwansa kuma za mu ci gaba da bincike tunda daya na hannunmu bayan mun kammala za mu tura shi Kaduna,” inji shi.