An ceto wanda ya yi kwana biyu cikin rami mai zurfin kafa 100
Ya kashe manyan macizai uku a cikin ramin Hukumar Kwana-Kwana a Jihar Arizona ta Amurka ta ceto wani mai hakar ma’adanai mai suna John Waddell mai shekara 60 wanda ya fada wa abokinsa cewa, idan har bai dawo gida ranar da ya kamata a ce ya dawo ba, wato ranar Talata to a […]
- Ya kashe manyan macizai uku a cikin ramin
Hukumar Kwana-Kwana a Jihar Arizona ta Amurka ta ceto wani mai hakar ma’adanai mai suna John Waddell mai shekara 60 wanda ya fada wa abokinsa cewa, idan har bai dawo gida ranar da ya kamata a ce ya dawo ba, wato ranar Talata to a yi cigiyarsa.
John Waddell ya tafi sana’arsa ce ta neman zinare inda ya fada cikin wani rami mai zurfin kafa 100 a wani yankin sahara inda aka samu sa’o’i ba tare da an samu masu aikin ceto a yankin ba.
An ceto John Waddell daga cikin ramin da dare ranar Laraba, wuni biyu daga lokacin da ya fada cikin ramin bayan da na’urar da ke taimaka masa wajen shiga ramin hakar ma’adanai ta tsinke wanda hakan ya sa ya zurma cikin kasan ramin.
Abokin Waddell mai suna Terry Shrader ya ce, ya kira Waddell ranar Litinin amma ya ce, yana tafiya a cikin sahara kusa da garin Aguila mai nisan mil 90 a Arewa maso Yamma na birnin Phoenid a Jihar Arizona don neman karfe mai daraja. Hukumomi sun ce, Waddell ya mallaki kadarori da ya nema shekara 20 da suka gabata.
Abokinsa Shrader ya bayyana wa kafar labarai ta NBC News cewa, ya damu matuka da bai san inda abokinsa yake ba har zuwa ranar Laraba. Amma sai aka yi sa’ar ya san inda zai nema shi kawai sai ya tafi nemansa kai-tsaye.
Shrader, ya ce, lokacin da aka zura na’urar da za ta taimaka wajen fitar da shi daga cikin ramin sai yajin muryar abokinsa yana ihu.
Shrader ya ce, a wajen neman abokinsa ya samu yankin da babu sabis din na’urar kiran waya da zai iya kiran lambar 911 ta neman taimako. Sai ya fara tsiyaya wa Waddel ruwa zuwa cikin ramin da kuma jiran wanda zai kawo dauki.
An nadi faifan bidiyon da ke nuna lokacin da jami’an agaji suke daura igiyar ceto Waddell daga cikin ramin da ya fada.
An yi nasarar ciro Waddell tare da jin rauni a jikinsa an kuma wuce da shi cibiyar kiwon lafiya ta Jami’ar Banner-Unibersity Medical Center a birnin Phoenid don yi masa jinyar raunin da ya samu a jikinsa.
Wani ma’aikacin asibiti ya bayyana wa majiyar NBC News cewa, ya karye a kafarsa amma an yi masa tiyata.
A cewar ma’aikacin asibitin “Mista Waddell na murnar saduwa da masoyansa kuma yana fatan zai warke ya dawo kamar bai shiga cikin wannan yanayin ba.
Shrader ya ce, Waddel ya fada masa cewa, sai da ya kashe manyan macizai uku a cikin ramin saboda gudun sarar macizan kafin a gano inda yake.