An ceto mutumin da aka daure shekara 15 a Sokoto

Salisu mai shekara 45 ya kasance a daure a gidan kawunsa na shekara 15 bisa zagin tabuwa

An ceto mutumin da aka daure shekara 15 a Sokoto

‘Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekara 45 da kawunsa ya daure shi shekara 15 bisa zagin ‘tabin hankali’ a Jihar Sokoto.

An ceto Salisu Muhamamd ne a kauyen Gidan Madi da ke Karamar Hukumar Tangaza, bayan makwabta sun kai wa gwamnati kara.

Mai ba Gwamna Aminu Tambuwar Shawara kan Hakkin Dan Adam da Hukumomin Agaji, Hajiya Ubaida Bello ta ce makwabta ne suka kai kara game da halin da Salisu ke ciki.

“Makwabtan sun zaci mutumin da kawun nasa ya daure ya dade da rasuwa saboda sun fi shekara 10 rabon da su gan shi; da suka gano halin da yake ciki sai suka yi gaggawar sanar da mu.

“Hakan ce ta sa muka yi wa gidan tsinke tare da ‘yan sanda da masu kare hakkin dan Adam da jami’an karamar hukumar, har da Shugaban Karamar Hukumar, muka kwato shi”, inji Ubaida.

Ta ce sun iske mata biyu a gidan ciki har da diyar wanda aka daure din mai shekara 19 da ta ce ba ta san iya tsawon lokacin da mahaifin nata ke a daure ba.

“Mun same shi cikin mawuyacin hali. A wurin yake fitsari da bayan gida ba tare da samun wata kulawa ba.

“Mutumin ya jeme har ba ya iya tafiya saboda tsabar rama. Idan suna maganar cewa tababba ne, me ya sa suka ajiye shi na tsawon lokaci ba su kai shi asibitin kwakwalwa a nema masa magani ba?”

Wasu shaidu sun ce wa wakilin Aminiya cewa kawun mutumin ne da ke zaune a kauyen da ke makwabtaka da su ya dauye shi.

Ubaida ta ce Karamar Hukumar ta kai Salisu asibitin kwakwalwa da ke Kware, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da binciken dauren shin da aka yi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce binciken da aka fara ya tabbatar cewa mutumin na fama da tabin hankali.

“Zuwa yanzu babu wanda aka kama da zargin aikata babban laifi kuma ba a kai ga tsare kowa ba tukuna”, inji shi.