An ceto wani yaro da aka sace, an kama mutum 4 Gombe

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

An ceto wani yaro da aka sace, an kama mutum 4 Gombe

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe, ta ceto wani yaro mai shekaru takwas da aka sace a Ƙaramar Hukumar Akko, tare da kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a sace shi.

An ceto yaron cikin ƙoshin lafiya, sannan an mayar da shi hannun iyayensa.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce mahaifin yaron, Alhaji Muhammadu Nabadara ne, ya kai rahoton ɓatan ɗansa a ranar 28 ga watan Yuni, 2026.

Ya bayyana cewa yaron ya fita daga gida da safiyar 27 ga watan Yuni, amma bai dawo ba, lamarin da ya sa iyayensa suka sanar da ‘yan sanda.

Bayan samun rahoton, jami’ai suka fara neman yaron tare da gudanar da bincike na sirri.

A ranar 29 ga watan Yuni, wani mutum ya kira iyayen yaron ya sanar da su cewar ya san inda yaron yake.

Sai dai bincike ya nuna cewa bayanin ƙarya ne da aka yi domin yaudarar jami’an tsaro.

Daga bisani, bayan samun sahihan bayanan sirri, ‘yan sanda suka kama wani da ake zargi mai suna Abdullahi Mohammed a unguwar Jauro Musa da ke Kumo, a Ƙaramar Hukumar Akko.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa shi da wasu mutum uku ne suka haɗa baki wajen sace yaron.

Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da Mohammed Magaji (shekaru 35), Sale Sale (shekaru 23), da Walida Ya’u (shekaru 18), duk mazauna unguwar Kagarawal.

‘Yan sanda sun ce an gano yaron a hannunsu, inda aka ceto shi cikin ƙoshin lafiya.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin saboda ƙwarewa.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da masu aikata laifuka.