An ceto wata mata da ranta kwana 6 da yin hatsari a cikin mota
Jami’an kiyaye hadurra na Arzona da ke Amurka sun bayyana wa hukumomi cewa, sun ceto wata mata mai kimanin shekara 53 wanda ta makale bayan yin hadari da kwana shida a wurin kuma ta ji mummunan rauni a cikin sahara, kusa da garin Wickenburg. Jami’an tsaron sun kai wa matar da ta makale ceton lokacin […]
Jami’an kiyaye hadurra na Arzona da ke Amurka sun bayyana wa hukumomi cewa, sun ceto wata mata mai kimanin shekara 53 wanda ta makale bayan yin hadari da kwana shida a wurin kuma ta ji mummunan rauni a cikin sahara, kusa da garin Wickenburg.
Jami’an tsaron sun kai wa matar da ta makale ceton lokacin da suke tafiya a babbar hanyar yamma da garin Wickenburg , kamar yadda kafar yada labarai ta AP ta sanar.
Wani ma’aikacin sufuri na Arizona, Zach Moralez ya ce, akwai abin da ya faru lokacin da suka ga wata katanga a rushe mai alamar hadari ya afkawa. Sai suka dakata a hanyar da tunanin cewa, za a iya samun mota daga kasan katangar da ta rushe.
Moralez, ya ce a lokacin da suka isa wurin da hadarin ya faru sai suka fara yekuwa da nufin ko wani zai amsa. Amma ba bu amsa, kamar yadda Moralez ya bayyana wa kafar yada labarai ta AP
Sai dai dan’uwan Moralez ya ce, da farko da ya halarci inda hadarin ya auku bai ga wanda ta yi hadarin a kusa da wata bishiya ba, amma duk da haka ya ci gaba bincike sai daga bisani aka gano abin da ya faru.
Da agajin jami’an tsaron Arizona suka gano wata mata mai kimanin shekara 53 a cikin motar da ta yi hadari, yayin da motar ta nannade ta, ta samu mummunan rauni sanadiyyar hadarin ta kuma kwashe kwana shida ba tare da ci ko sha ba a cikin sahara.
Moralez ya ce, matar da ta yi hadarin tana cikin wani yanayi da ba zata iya motsa wa ko ina ba. Daga bisani muka fara yi ma ta tambayoyi kamar haka: kwana nawa ki ka yi anan? Kina jin wani ciwon jiki?
Duk da yanayin raunin da matar ta samu ta yi kokarin bude ido ta amsa tambayoyin da ake yi mata. Moralez ya ce, matar ta yi matukar datti sanadiyyar kwanan da take yi a cikin turbaya sannan tana cikin wani yanayi na dimuwa sanadiyyar hadarin mota.
Bayan kammala tambayoyin da jami’an suka yi mata an fitar da ita daka kasar zuwa wani asibitidon yi mata jinya. Saboda a binciki lafiyar ganin ta kai kwana shida ba tare da cin abinci ba.
Bayan farfadowar matar ta bayyana yadda ta yi mummunan hadari lokacin da motarta ta kauce hanya ta yi cikin sahara wanda ya zama abu mai wahala kafin a galno cewa, akwai mai rai a wurin.
Kakakin jami’an tsaron Kuentin Mehr ya ce, matar dai taki amince wa da ta bayyana wa manema labarai halin da take.
Daraktan jami’an tsaron Kanal Frank Milstead ya jinjina wa jami’an sufurin da masu kiyaye hadduran na ceto rayuwar matar.