An ci direba tarar Naira miliyan 96 kan gudun wuce kima

Hakika na yi nadamar wannan laifi da na aikata.

An ci direba tarar Naira miliyan 96 kan gudun wuce kima

Direba yana tsala gudu a mota

An ci wani direba tarar Yuro 121,000 wato Dala dubu 129 da 544 (kimanin Naira miliyan 96 da dubu 251 da 192) a canjin Naira a kasuwar bayan fage bayan da aka kama shi da laifin gudun da ya wuce kima.

Direban Mista Wiklof yana gudun kilomita 82 ne a cikin awa daya wurin da aka ce kada mota ta yi gudun da ya wuce kilomita 50 a awa daya, inda ’yan sanda suka dakatar da shi, suka rubuta masa takardar tuhuma.

Bayan tarar an dakatar da lasisin tukinsa na tsawon kwana 10, kuma bincike ya nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kama Wiklof da laifin gudun wuce kima ba a kasar.

Kafar labarai ta AP ta ce jaridar NyaAaland ta kasar da ta bayar da labarin ta ce, an taba kama shi a shekarar 2018 inda aka ci tararsa Yuro dubu 63 da 680 (Dala dubu 68 da 176), bayan shekera 5 aka sake cin tararsa Dala dubu 102 kafin wannan tara ta baya.

“Hakika na yi nadamar wannan laifi da na aikata,” in ji Mista Wiklof a hirarsa da jaridar.

Mista Wiklof shi ne shugaban wani kamfani da ke harkar sufuri da kuma wasu harkokin kasuwnci a kasar da suka hada da bayar da hayar jirage masu saukar ungulu da saye da sayar da filaye da gidaje.

Tarar da mutum zai biya a kasar ana aunata ce da karfin aljihun mai laifi, wato daidai ruwa, daidai kurji.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina