An ci gaba da gumurzu bayan cikar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan

Kashi 20 kadai ne da ma’aikatun kiwo lafiya ke aiki a birnin na Khartoum.

An ci gaba da gumurzu bayan cikar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan

An ci gaba da gwabza rikici a babban birnin Sudan Khartoum a ranar Lahadi, bayan karewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon awa 24 da bangarorin da ke rikici da juna suka cimma.

Yarjejeniyar ta taimaka wajen bai wa mazauna birnin Khartoum damar fita don sayen kayan abinci da kuma isar da kayan agaji wasu bangarori.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewar minti 10 bayan karewar wa’adin yarjejeniyar a jiya Lahadi, aka fara jin karar fashe-fashe a birnin da ya kwashe tsawon Asabar ba tare jin su ba.

An kuma ci gaba da gwabza fadan a yankin Darfur, inda kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka bayyana damuwa a game da rincabewar al’amura.

A Juma’ar da ta gabata ma dai shugaban tawagar jami’an agaji na Red Cross da ke Sudan, Alfonso Verdu Perez ya yi gargadin cewa kashi 20 kadai ne da ma’aikatun kiwo lafiya ke aiki a birnin na Khartoum inda a nan ne fadan ya fi kamari.

A baya an sha cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin masu rikici da juna, ciki kuwa har da wacce Amurka ta yi barazanar sanya wa Janar Janar din takunkumi amma sai dai haka bata cimma ruwa ba.

Tun bayan faro rikicin a tsakiyar watan Afrilun da ya gabata, mutane kusan dubu daya da dari 8 ne suka rasa rayukan su, yayin da kusan mutane miliyan biyu suka bar muhallin su ciki kuwa har da mutane dubu dari 476 da ke gudun hijira a kasashe da ke makwafta da Sudan.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja