An ci gaba da kashe-kashe duk da dokar hana fita ta sa’a 24 a Filato

Mahara sun yi wa garin Mangu kawanya, suna harbin duk wanda suka gani, suna kuma kona gidaje

An ci gaba da kashe-kashe duk da dokar hana fita ta sa’a 24 a Filato

Rahotanni daga Filato na nuni da cewa an ci gaba da kashe-kashe da kone-kone a garin Mangu, duk kuwa da dokar hana fita tsawon sa’a 24 da gwamnatin jihar ta kafa.

Mazauna Karamar Hukumar Mango sun ce mahara dauke da makamai sun yi wa garin Mangu kawanya suna harbin duk wanda suka gani, suna kuma kona gidaje ciki har da wata makarantar Islamiyya a kan titin Gindiri.

Wani mazunin garin, ya shaida wa wakilimu cewa, “Da misalin kafe 9:30 na safe mahara dauke da muggan makamai suka shigo suna harbin duk wanda suka gani.

“Sun kashe mutasni sun kona gidaje da Makarantar Sunnah Islamiya; A halin da ake ciki sun fi karfin jami’an tsaron da ke garin Mangu. A halin yanzu ’yan bindiga ne suka zagaye mu.”

Wakilimu ya nemi samun karin bayani daga kakakin rundunar soji ta Operation Safe Haven, wadda ke samar da tsaro a jihar, Kyaftin Oya James, amm har yanzu bai samu ji daga gare shi ba.

A ranar  Talata Gwamna Caleb Mutfwang ya sa dokar hana fita tsawon sa’a 24 a karamar hukumar sakamakon ci gaban rikicin wanda ya samo asali tun alokacin bukukuwan Kirsimeti.