An ci tarar bazawara N55,000 saboda zuwa kabarin mijinta da kare

Bazawarar ta ce an sa ta zama kamar wata mai laifi

An ci tarar bazawara N55,000 saboda zuwa kabarin mijinta da kare

Lynda Martin tare da karen nata

An ci tarar wata bazawara Fam 100 (kimanin Naira dubu 54 da 671 da kwabo 91 saboda ziyartar kabarin mijinta tare da kare tana kira ga majalisar dokokin kasar ta yi watsi da dokar hana karnuka zuwa makabarta.

Bazawarar mai suna Lynda Martin ta ce, an sa ta zama kamar wata mai laifi a birnin Herne Bay da ke Birtaniya.

Wata mai suna Kent ce ta zama ta farko da aka ci tararta saboda karya dokar, tun daga shekarar 2017.

Matar mai shekara 67 tana yawaita ziyartar makabartar tare da karenta mai suna Megan tunda aka binne mijinta mai suna Niall Willis mai shekara 81 a watan Afrilun bara.

Karen mai shekara 12 yana gefenta aka yi jana’izar Niall.

Matar ta ce: “Megan na kan gaba kuma a karkashin kulawa. Ita ce tawa abokiyar zama da kuma goyon bayana.

“Ban san abin da zan yi ba, ba tare da ita ba. Ina tsammanin tilasta wa jami’an tsaro sun fi kama irin su maimakon masu aikata laifuffuka na gaske – ya kamata su tashi su kama batagari – maimakon farautar mai karamin karfi.” Kuma ta nemi a yi watsi da hukuncin.

Wani mai magana da yawun Lynda Martin ya ce, Majalisar Yankin Canterbury ta sassauta wa Misis Martin hukuncin, amma ta ce ba za ta iya jingine dokar ba. Amma ta ce, lokacin da majalisa ta gaba ta sake duba haramcin, za su ci gaba da tuntubar jin ra’ayin jama’a’ don duba ko suna da goyon bayan hakan.

Wani jami’in kamfanin da ke tallafa wa qananan hukumomi mai suna Kingdom LA Support ne ya bayar da sanarwar.

A baya dai hukumar ta dauki aikin ne a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, inda ake yawan sukar jami’anta da cewa, suna yawan sukar bazawarar.

Wani abin tunawa a wannan lokaci an ga ma’aikata suna biyan wadansu mata da ba su da aure ko suka rabu Fam 160 don sharar gida bayan sun bar dimbin dukiya a baya kafin su zama zaurawa.