An ci tarar dan majalisa saboda ya yi fitsari cikin mutane
Kotu ta ci tarar wani dan majalisa a kasar Uganda saboda ya yi fitsari a cikin mutane. Kotun da ke zama a birnin Tarayyar kasar ta sa Abraham Abiriga ya biya 40,000 na kudin Uganda wanda yake dai dai da Dalar Amurka 10 saboda laifin da ya yi ya janyo cece-kuce a cikin jama’a. Dan […]
Kotu ta ci tarar wani dan majalisa a kasar Uganda saboda ya yi fitsari a cikin mutane. Kotun da ke zama a birnin Tarayyar kasar ta sa Abraham Abiriga ya biya 40,000 na kudin Uganda wanda yake dai dai da Dalar Amurka 10 saboda laifin da ya yi ya janyo cece-kuce a cikin jama’a. Dan majalisar kuma tuni ya biya tarar.
An dauki hoton Abiriga a karshen watan Satumba yana fitsari a kusa da kofar ma’aikatar kudade, inda hoton daya jawo cece kuce a kafafen yada labarai wanda ya jawo aka kama shi aka maka shi a kotu.
New vision portal su ka yi rahoton cewa mai kara ya tabbatar da cewa Abiriga ya karya dokar birnin Kampala ta shekarar 2016.
A lokacin afkuwar abin, ya kare kansa da cewa fitsarin ne ya matseshi sosai shi ya sa ya yi wannan aika aika.