An ci tarar gidan abinci a Connecticut kan sanya alamar hana kare yin fitsari a harabarsa
Allon gargadi ga mutane cewa kada su bar karnukansu su yi fitsari a harabar wani gidan abinci a garin Connecticut da ke Amurka musamman a kusa da tukunyar filawa ya janyo wa mai gidan abinci tarar Dala 250. Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ce mai gidan abincin Duc Nguyen, ya shaida wa kafar labarai […]
Allon gargadi ga mutane cewa kada su bar karnukansu su yi fitsari a harabar wani gidan abinci a garin Connecticut da ke Amurka musamman a kusa da tukunyar filawa ya janyo wa mai gidan abinci tarar Dala 250.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ce mai gidan abincin Duc Nguyen, ya shaida wa kafar labarai ta New Haben Independent cewa, yana mamakin yadda jama’a ke barin karnukansu suna fitsari a cikin tukwanen fulawa da aka shuka.
Da farko na yi tunanin allon da ke dauke da rubutun gargadi wata hanya ce da za ta sanya masu kiwon karnuka kyamar barin karnukansu su fitsari a wurin da aka shuka fulawa. Rubutun gargadin na cewa: ‘Gargadi ga masu karnuka, wannan tukunyar fulawar za a iya yin fitsari a biya a ciki. Za a iya biya a cikin gidan ko kuma a bar adireshin gida.’
Wani jami’in hukumar muhalli Honda Smith, ya ce Nguyen ya saba dokokin birnin biyu na janyo wa jama’ar garin matsaloli tare da cin tararsa. Sai dai Nguyen yana shirin daukaka kara.