An ci tarar Kano Pillars miliyan daya kan kutsen magoya baya cikin filin wasa
Hukumar Kula da Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) a ranar Litinin ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayanta suka yi a filin wasa. Hukumar ta dai ta ce ta dauki matakin ne saboda kutsen da ’yan kallon suka yi a wasan da kungiyar ta fafata da takwararta ta Rivers United a […]
Hukumar Kula da Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) a ranar Litinin ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayanta suka yi a filin wasa.
Hukumar ta dai ta ce ta dauki matakin ne saboda kutsen da ’yan kallon suka yi a wasan da kungiyar ta fafata da takwararta ta Rivers United a ranar Lahadin da ta gabata.
- An yanke wa likitan da ya yi wa ’yar uwar matarsa fyade daurin rai da rai
- Yadda muka rayu a hannun mayakan Hamas —’Yar Isra’ilar da aka sako
An tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ketara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 da fara wasa a karawar da suka yi da kungiyar ta Rivers United a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Bayan nazarin rahotanni daga jami’an wasan, Hukumar NPFL ta tuhumi kungiyar da laifin karya doka mai lamba B13.18.
Don haka an umurci kulob din da ya biya tarar cikin kwana 14 kuma ya ja kunne kan hakan.
Gaza yin hakan, a cewar NPFL, zai zamo tamkar ci gaba da saba wa dokokin hukumar.