An ci tarar ta Naira dubu da 500 a kan fasa idon yaro
Malam Abubakar Atathiru mahaifin Idris Abubakar yaron da ake zargin wata mata wacce suke haya a gidanta, mai suna Murjanatu Sani da laifin tsiyayar masa da idanuwa sakamakon jifan sa da ta yi da bulugari a ranar 5/12/12, ya bayyana cewa bai gamsu da hukuncin da alkali ya yanke akan matar ba, wato tarar Naira […]

Malam Abubakar Atathiru mahaifin Idris Abubakar yaron da ake zargin wata mata wacce suke haya a gidanta, mai suna Murjanatu Sani da laifin tsiyayar masa da idanuwa sakamakon jifan sa da ta yi da bulugari a ranar 5/12/12, ya bayyana cewa bai gamsu da hukuncin da alkali ya yanke akan matar ba, wato tarar Naira dubu da 500 ko zaman kaso na wata daya.
“A gaskiya ban ji dadin hukuncin da alkali ya yanke wa wanann mata ba. Ta yaya za a ce duk girman laifinta amma yanke mata hukuncin daurin wata daya a gidan kaso, ko tarar Naira 1500? Idan har na amince da wannan hukunci ikrarin da wannan mata take yi na cewa, ta doki dana Idris ta doki banza babu abin da za a yi mata, to zai tabbata ke nan. Ina so ko ba komai a nuna wa wannan mata kuskurenta don ya zama darasi ga sauran masu hali irin nata. Ido fa ba abin wasa ba ne, domin ba a sayar da shi a kasuwa” a cewarsa, cikin hirar da ya yi da .
Ya ce duk da kotu ta ba su damar yin sulhu a tsakaninsu wajen biyan diyya, shi ba zai nemi bangaren masu laifi ba, amma idan sun neme shi kafin wa’adin makonni biyu da ya diba musu to zai iya zama da su a teburin sulhu, idan dai har sun shirya biyansa wani abu mai kauri. “Dama ni tun farko ban ki mu yi sulhu ba, amma wulakanci da rainin hankalin da aka nemi nuna min shi ya sa na kai maganar gaban kuliya. Ta yaya za a ce a tsiyayar da idan yaro sannan wai a ce za a dauko Naira dubu 20 a ba ni, wanda ko kudin maganin da na kashe akan yaron ya fi haka. Abin da nake cewa shi ne dole mutanen nan su san abin da za su yi wa yaron nan, domin su suka jawo masa halin da yake ciki” Inji shi.
Uban yaron ya bayyana cewa idan har wa’adin wannan lokaci ya cika bai ji daga bangaren masu laifi ba, to zai daukaka kara kamar yadda alkalin da ya yanke wancan hukunci ya ba su dama, domin kuma a nema masa hakkinsa.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su taimaka masa wajen kwato hakkin dansa daga wurin mutane da ke kokarin tauye masa. Yadda aka yi shara’ar
A makon da ya gabata ne aka yanke hukunci game da shari’ar nan da ake yi tsakanin iyayen wani yaro Idiris Abubakar dan kimani shekaru 12, wanda ake zargin wata mata wacce suke haya a gida daya ta yi sanadin tsiyayar masa da idanu, ta hanyar jifan sa da bulugari.
Kafin yanke hukuncin bayan mai gabatar da kara Inspecta Yusuf Bello ya karanto takardar kara, alkalin kotun, Malam Habibudden Sulaiman Sharifai ya nemi jin ta bakin wacce ake kara, wato Murjanatu Sani da ta bayyana wa kotu abin da take so, inda ta roki kotu da ta yi mata sauki wajen hukunci tunda wannan laifi da ake zargin ta da shi ba da gangan ta aikata shi ba , a cewarta abu ne na tsautsayi.
A hukuncin da Alkalin ya yanke ya bayyana cewa, kotu ta samu Murjanatu Sani da laifin sanadin mummunan rauni ga Idris Abubakar sakamakon jifansa da bulugari da ta yi a ranar 5/12/2012, a gidansu da ke unguwar Tarauni, wanda hakan ya jawo idon ya yi ta zubar jini, har a karshe ya tsiyaye bayan an kai shi asibiti, wanda hakan laifi ne da ya saba wa sashe na 159 na kundin shari’ar Musulunci ta shekarar 2000. Sakamakon haka kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata daya a gidan kaso ko biyan tarar Naira dubu da 500.
Alkali Habibudden Sulaiman Sharifai ya ce “Kotu ta tabbatar miki da wannan laifi ne bisa samun shaidun mutum uku da aka yi da kuma kasa kare kanki da kika yi daga wannan laifi da ikrarin da kika yi tare da rahoton likita. Haka kuma a lokacin da shaidun mai gabatar da kara suka bayyar da shaida a gaban kotu kuma a gabanki ba ki raunata shaidarsu ba. “saboda kasancewar wannan shi ne laifi na farko da ya bayyana da rokon da kika yi na hore ki da daurin wata daya a karkashin 167(a) na kundin shari’ar “Penal Code.” Kuma har ila yau na hore ki da biyan ramko ga Idris Abubakar kamar yadda aka bayyana a karkashin 163 (a)(b) a cikin kundin shari’ar “Penal Code” ko wata masalaha da kuka cimma a tsakaninku da mahaifinsa na ramko.’ Inji Alkalain.
Ana iya daukaka kara
Alkalin ya bayyana cewa amma idan mai kara da wacce ake kara sun kasa cimma wata masalaha, to ana iya shigar da kara gaban shari’a don kotu ta bincika, idan kotu ta bincika ita kuma sia ta karba masa hakkinsa. A karshe kotun ta yi umarni da cewa dukkanin wanda bai ji dadin hukuncin da kotun ta yanke ba, ya daukaka kara a kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci cikin kwanaki 30 daga ranar 10/10/13.