An ci tarar tsoho saboda carar zakaransa
An ci tarar wani tsoho mai kimanin shekara 83 Yuro 166, kwatankwacin N77,304 bayan makwabtansa sun kai karar sa kan wani zakaransa da ke takura musu da cara kullum da safe. ‘Yan sanda kasar Italiya sun kama tsohon da laifin karya dokar ajiye dabbobi ta kasar da ta tanadi ajiye su akalla tsawon mita goma […]
An ci tarar wani tsoho mai kimanin shekara 83 Yuro 166, kwatankwacin N77,304 bayan makwabtansa sun kai karar sa kan wani zakaransa da ke takura musu da cara kullum da safe.
‘Yan sanda kasar Italiya sun kama tsohon da laifin karya dokar ajiye dabbobi ta kasar da ta tanadi ajiye su akalla tsawon mita goma daga makwabta.
To sai dai babban dalilin cin tarar tasa shi ne wani zakaransa da ya ke kira da Carlino, yana fara cara tun misalin karfe 4:30 na Asuba, wanda hakan ke matukar takura wa makwabtan Mista Angelo.
A kan haka ne ’yan sanda bayan karbar tarin korafe-korafe suka sanya wa zakaran ido, wanda bayan sun tabbatar da zargin ne suka yanke wa mai shi hukuncin biyan tarar.
“Ba ni da ta cewa a kan lamarin, babu bukatar yin haka. Kamata ya yi su sanar da ni a kan dokar tun da farko, ba ni da masaniya a kan ta,” inji Mista Angelo wanda tsohon magini ne, a hirarsa da wata jaridar kasar.
Magajin garin na Castiraga Vidardo, Emma Perfetti ya shaida wa ’yan jarida cewa mahukuntan garin ba su da wani zabi face yanke masa wannan hukuncin bayan karbar dimbin korafe-korafe daga makwabtan wanda ake zargin.
Akwai dai yiwuwar ’yan sanda sun tura jami’ansu zuwa gidan mutumin tun dare sannan suka tabbatar da cewa zakaran na fara cara tun misalin 4:30 na asuba har zuwa 6:00 na safe kafin yanke hukuncin.