An ci tararsa don yin bikin ranar haihuwarsa
A makon jiya ne aka ci wani mutum tara a kasar Tajikistan bayan ya karya dokar hana yin bikin tunawa da ranar haihuwa a bainar jama’a, kamar yadda kafar yada labarai na the Top TJ news ya bayyana. Mutumin mai suna, Isayeb Amirbek, ya wallafa hotunan shagulgulan ne a shafinsa na Facebook, wadanda suke nuna […]
A makon jiya ne aka ci wani mutum tara a kasar Tajikistan bayan ya karya dokar hana yin bikin tunawa da ranar haihuwa a bainar jama’a, kamar yadda kafar yada labarai na the Top TJ news ya bayyana.
Mutumin mai suna, Isayeb Amirbek, ya wallafa hotunan shagulgulan ne a shafinsa na Facebook, wadanda suke nuna lokacin da yake yanka kek. Kuma da su aka yi amfani a matsayin hujja wajen hukunta shi. An dai ci shi tarar Dala 634 (kimanin naira dubu dari da 26 ke nan).
Kamar yadda wani tanadin dokar kasar ya yi. An haramta yin bikin tunawa da ranar haihuwa a bainar jama’a, sai dai a boye a cikin gida.
Ba dai Mista Amirbek ne mutumin farko da zai karya dokar ba, an ruwaito cewa a bara wasu mutane sun karya dokar har 394. An dai kafa dokar ne domin kare al’adun kasar da kuma kauce wa kashe makudan kudi lokacin bikin.
kasar wadda ta ke nahiyar Asiya, tana da jama’ar da suka kai miliyan takwas wadanda galibinsu Musulmi ne. Kuma ta samu ‘yancin kanta ne a shekarar 1992 bayan rushewar Tarayyar Sobiet.