Tallar Crypto ya ja wa tauraruwar shirin talabijin tarar Dala miliyan1.26
Amurka ta ci Kim Kardashian tarar Dala miliyan 1.26 saboda tallata kudin Crypto a shafinta na Instagram
Hukumar hadahadar hannun jari ta Amurka (SEC), ta ci tarar fitacciyar mai fitowa a shirin talabijin, Kim kardashian Dala miliyan 1.26, bisa kin bayyana biyan ta Dala dubu 250 da kamfanin kasuwancin Crypto na EthereumMax ya yi domin tallata shi.
Kim Kardashian dai ta tallata kudin yanar gizon crypton ne a matsayin sahihin hanyar hannun jari a shafinta na Instagram a watan Yunin 2021.
- Ambaliyar Jigawa: Sufurin kwale-kwale ba bisa ka’ida ba na kara cin rayuka
- Ambaliya ta kara tasar wani kauye a Jigawa
A shekarar ce fitattaun mutane da dama a Amurkan suka fara tallata kudaden Crypto, kafin Hukumar SEC din ta gargadi masu zuba jari kan sayen sa don kawai ya samu goyon bayan wani fitaccen mutum.
A cewar hukumar kamfanonin Crypto da dama a kasar na da tarihin biyan mutanen cikin sirri, da sharadin ba za su bayyana wa duniya cewa sun biya su don tallata su ba, sai don gamsuwa da kasuwancin.
Cikin wata sanarwar da Shugaban Hukumar ta SEC, Gary Gensler ya fitar, ya ce tarar da aka ci Kim Kardashian ta zama izina ga sauran fitattun mutane a aksar, kan muhimmacin bayyana wa jama’a lokacin da kuma nawa aka biya su don tallata kadarorin Crypton.
A nasa bangaren, Lauyan Kim mai suna Patrick Gibbs, ya ce suna farin ciki da aka warware wannan batu da SEC ba tare da wata matsala ba, kuma yarjejeniyar da suka cimma, ta ba ta damar ci gaba da harkokin kasuwancinta.