An cinna wa fadar Sarki Sanusi II wuta a Kano

Ana zargin wasu da cinna wa fadar wutar cikin dare.

An cinna wa fadar Sarki Sanusi II wuta a Kano

Ana zargin wasu da bin dare tare da cinna wa fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II wuta.

Wata majiya daga fadar wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 11 na dare.

Majiyar ta ce ɗaya daga cikin fadar Sarkin da ke Kofar Kudu, inda Sarki ke zaman kotu duk ranar Litinin ta lalace sosai sakamakon wutar.

“Kofar Kudu ce ka san tana da hanyar shiga ta ciki, yayin da ta ke da ƙofa ta waje. An ɓalle makullin ƙofar, abin da ake zargi sun kunna wutar sannan suka rufe ƙofar.

“Ya zuwa yanzu karagar mulkin, na’urar sanyaya ɗaki da sauran kayayyakin amfani duk sun ƙone.”

Da aka tuntuɓi kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi kan lamarin, ya ce ba su da masaniyar faruwar lamarin domin babu wani kiran waya da suka samu game da hakan.

Kazalika, Shugaban Ma’aikatan Fadar Sarkin, Munir Sanusi Bayero, Dan Buram Kano, cikin wata sanarwa ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Da safiyar ranar Asabar 13 ga watan Yuli, 2024 wuta ta tashi a kotun Sarki da ke Ƙofar Kudu. Ba a samu wanda ya ji rauni ba kuma ɓarnar da wutar ta yi kaɗan ce.

“Fadar tana ɗaukar duk matakan da suka dace don tabbatar da tsaron mazauna cikinta. Kuma muna binciken musabbabin tashin gobarar tare da ɗaukar matakai don hana faruwar hakan a gaba.”

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC