‘An cire al’aura da idon gawar mahaifiyarmu a asibitin Gombe’
Iyalan sun ce babu tabo suka kawo ta, amma sai suka ga an cire wasu sassan jikinta
’Ya’ya da ’yan uwan wata mamaciya da ta rasu a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe sun yi zargin an cire wasu sassan jikinta bayan ta rasu a asibitin.
Mutanen dai sun gudanar da boren nuna rashin amincewarsu a gaban mashigar asibitin ranar Talata, suna kiran a dawo musu da sassan jikin gawar matar mai suna Halima Ibrahim mai shekara 61 da aka cire.
- INEC ta sanar da ranar zaben Gwamna a Edo da Ondo
- Za mu tsayar da komai cak a Najeriya ranar 3 ga watan Oktoba – ’Yan kwadago
Da take zantawa da manema labarai a a kofar asibitin, diyar marigayiyar, Hannatu Aminu ta ce sun kai mahaifiyarsu ne jinya a asibitin a lokacin da ta fara fuskantar matsalar daukewar numfashi a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 4:00 na yamma.
Ta ce lokacin da suka kai ta asibitin, babu wani tabo ko ciwo a jikinta, inda ta rasu kashegari Asabar da karfe 5:00 na yamma.
Hannatu, tace kafin rasuwar mahaifiyar tasu, an shaida musu cewa za a sanya mata iskar shaka ta oxygen, saboda numfashinta ne daddaukewa.
Sai dai ta ce kafin a kai ga haka, marigayiyar ta ce ga garinku nan. A nan ne suka kai gawarta ɗakin adana gawarwaki na asibitin.
Ta kuma ce bayan gawar ta kwana biyu a dakin gawarwakin sai aka turo masu daukar gawar don yi mata wanka a ranar Talata.
Hannatu ta ce an tafi da ita gida, amma kafin aje Coci, da suka bude ta sai suka tarar an cire ma ta ido daya.
Ta ce da ta yi magana sai aka ce ta yi shiru. Da aka je coci suka tayar da maganar cewa mahaifiyarsu ta rasu ba tabo, amma sai ga shi an cire mata ido daya da kuma al’aurarta.
A cewar Hannatu, lokacin da suka dauko gawar mai gadin dakin gawarwakin ya shaida musu cewa ba sai sun mata wanka ba an riga an yi mata.
A nan ne ta ce sun tambayi me yasa mai gadin zai yi mata wanka kasancewarta ba ’yar uwarsa ba.
“Bayan mun tabbatar da an cire mata ido daya mun tarar gabanta ma an yanke shi an cusa auduga hakan ne ya tunzura mu yin bore a kan a dawo mana da sassan jikin ta da aka cire,” in ji Hannatu.
Da wakilinmu ya tuntubi hukumar gudanarwar asibitin Mataimakin Shugaban asibitin, Farfesa Adamu Bojude ya tabbatar da cewa mamaciyar ta kwanta jinya a asibitin kuma ta rasu.
Ya kuma ce yanzu haka ’yan uwan mamaciyar da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta CAN da likita daga bangaren iyalanta da jami’an tsaro sun je asibitin don gudanar da bincike a kan lamarin.
Sai dai ya ce ba su ji dadin yadda lamarin ya faru ba, inda ya ce za su tabbatar an hukunta duk wanda aka tabbatar yana da hannu a cikin zargin.