An cire idanu da sassan jikin wata mata a Mubi

An kashe wata mata da ake kyautata zaton mai tabin hankali ce kuma aka cire idanunta a Unguwar Bolori da ke karamar Hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa a Lahadin da ta gabata. Aminiya ta gano cewa mutanen unguwar sun shiga rudani lokacin da suka ga gawar matar, wadda a cewar wani mutum da […]

An cire idanu da sassan jikin wata mata a Mubi
An cire idanu da sassan jikin wata mata a Mubi

An kashe wata mata da ake kyautata zaton mai tabin hankali ce kuma aka cire idanunta a Unguwar Bolori da ke karamar Hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa a Lahadin da ta gabata.

Aminiya ta gano cewa mutanen unguwar sun shiga rudani lokacin da suka ga gawar matar, wadda a cewar wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa,  mutane da dama ba su iya tsayawa sun kalli gawar ba, saboda irin rashin imani da aka  yi wa mata.

Mutumin ya kara da cewa matar tana da tabin hankali sannan bisa ga yadda aka kwakule idanuwanta da yanke nonuwanta da al’aurarta, alamu ne da ke nuna cewa matsafa ne suka yi wannan aika-aikar.

Ya ce mai tabin hankalin ta kasance cikin zaman lafiya da makwabtanta kuma shekarunta ba za su wuce ashirin ba. Ya ce wannan shi ne karo na farko da suka fuskanci irin wannan abin tsoratarwar a unguwar, sannan ya gargadi mutane da su bude idanunsa wajen lura da irin mutanen da suke shigo musu unguwanni, musamman a wannan lokacin da zaben 2019 ya gabato.

Da aka tuntubi Mukaddashin Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamawa, DSP Habibu Musa game da lamarin, ya ce ba ya da masaniya kan faruwar haka. Sai dai wani dan sanda a Mubi ya tabbatar da faruwar hakan.

Hukumar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta yi kira ga jama’a su lura da ’ya’yansu, saboda yawan kukan da ake kai musu na batan yara kanana a jihar.