An cire matacciyar tsoka laba 3 a hannuwan tsohon sojan da ya yi wa kansa allurar man shafawa

Wani tsohon soja mai suna Kirill Tereshin da ake wa lakabi da  Popeye  ya yi ma kansa allura da man shafawa wacce ta haifar masa da matsalar da ta sanya tsokar hannunsa ta mutu lamarin da ya sanya sai da aka yi masa tiyata don a ceto rayuwarsa.  An gargadi Kirill Tereshin, mai shekara 23  […]

An cire matacciyar tsoka laba 3 a hannuwan tsohon sojan da ya yi wa kansa allurar man shafawa

Wani tsohon soja mai suna Kirill Tereshin da ake wa lakabi da  Popeye  ya yi ma kansa allura da man shafawa wacce ta haifar masa da matsalar da ta sanya tsokar hannunsa ta mutu lamarin da ya sanya sai da aka yi masa tiyata don a ceto rayuwarsa.  An gargadi Kirill Tereshin, mai shekara 23  cewa zai iya mutuwa in har ba a yanke masa  hannuwan biyu ba saboda cutar da ta shafe su ta dajin tsoka.

Masu aikin tiyata a asibitin Jami’ar Moscow State Medical Unibersity da ke Mosko, Babban Birnin Kasar Rasha sun ce sun cire matacciyar tsoka mai nauyin laba 3 da kuma lita uku na man shafawa da ta daskare a cikin hannuwansa.

Babban likitan da ya jagoranci aikin fidar mai suna Dmitry Melnikob ya ce shi da ayarinsa sun kammala daya bisa uku ne kawai na wannan babban aiki. Kuma akalla za a yi tiyata sau uku a gaba kafin a samu nasarar kwashe duk  man shafawa mai kama da basilin da ke jibge a cikin damatsansa.

Mutumin wanda yake kokarin mayar da kansa dunkulallen kato ta hanyar motsa jiki, wata mai fafitikar kare ’yancin masu fama da wahala bayan an yi masu tiyatar fata, ta saka wani faifan bidiyo da ke nuna yadda tsokar take bayan da aka yi aiki na farko, inda a ciki aka gan shi yana tambayar likitan “Yaya yawan tsokar da aka cire daga jikina?” Shi kuma mai tiyatar ya fada masa cewa  “Matsalar ita ce ta wannan man shafawar da ka yi wa kanka allura da shi kuma ya gudana cikin tsokar hannuwanka ya kuma kashe tsokar.”

‘Ta riga ta mutu.” Ya ci gaba da cewa “Mun riga mun yi wajen rubu’in gyaran.”

An fada wa Kirill cewa zai iya motsa kafadunsa amma fa duk tsokar hannuwansa za a cire ta. Alana, wacce ta taimaka wajen neman taimakon sama masa kudin da aka yi masa wanan tiyata ta ce “Za mu yi bakin kokarinmu wajen ganin mun tallafa wa wannan matashi.

Tsohon sojan tun kafin fara aikin cire tsokar ya fada mata cewa “A shirye nake, ba na ma jin tsoro.” Dokta Melnikob ya fada masa: “Man shafawar ya karade tsoka da fatar, kuma dole a cire shi baki daya, amma kuma dole mu tabbatar aikin namu bai taba lafiyar jijiyoyi ba da kuma wasu sassa.”

Ya ci gaba da cewa “Ba a yi man shafawa ba don a yi allura da shi, ana amfani da shi ne kawai a kan fata. Amma ga Kirill  ya yi  wa kansa allurar wajen lita uku a kowane dantse. Don haka ya bi cikin tsokarsa ya daskarar da jijiyoyin jininsa  ya kashe masa tsokar hannuwan kuma ya cure ta ta yi tauri kamar itace.  Wannan ya sanya yake fama da zazzabi da  radadi tare da kasala.

“Kirill ya yi sa’a ganin cewa cutar ba ta bazu zuwa wasu sassan jikinsa ba,” inji likitan.

Dokta Melnikob ya ci gaba da ce “Man yana iya shafar lafiyar jikinsa gaba daya musamman  kodarsa.  Na tabbata bai san illar abin da ya aikata ba.”

Kafar labarai ta metro.co.uk ta ce, a kasar Rasha, tiyatar fata da ta kunshi matsalar man shafawa tana kara karuwa, saboda yawaitar samun masu yi wa kansu allura a nono da mazaunai da kuma fuska .

 

NAJERIYA A YAU: Haƙiƙanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Edo

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu