An cire wa ’yar Sin mai shekara 70 dutse mai nauyin kilo 1.19 a mararta
Wata tsohuwa ’yar kasar Sin mai shekara 70 da ake kira Zhang Guolun ta yi fama da cutar mafitsara a mararta, tun a shekarar 1973. Sai a kawanan nan likitoci suka yi mata aiki a marar, inda suka ciro wani dutse mai tsawon sentimita 14 da nauyin kilo guda da digo 19.“Dutsen da ke damfare […]
Wata tsohuwa ’yar kasar Sin mai shekara 70 da ake kira Zhang Guolun ta yi fama da cutar mafitsara a mararta, tun a shekarar 1973. Sai a kawanan nan likitoci suka yi mata aiki a marar, inda suka ciro wani dutse mai tsawon sentimita 14 da nauyin kilo guda da digo 19.
“Dutsen da ke damfare a mararta mai launin fatsi-fatsi ya bai wa likitoci mamaki. “Na dade ina aikin likitanci tsawon shekaru, amma ban taba ganin irin wannan dutsen a mara ba.” A cewar Dokta du Liangshan, wanda ya yi fidar ciro wannan dutse daga marar Zhang. “Wannan shi ne dutse mafi girma da na taba ganin an ciro daga mara, domin wanda na taba gani bai wuce girman kwai ba,” inji shi.