An ciro almakashin tiyata da ya shekara 18 a cikin wani
Bayan shekara 18 da yi wa wani mutumin kasar Bietnam tiyata a wani asibiti sakamakon yawan ciwon ciki da yake fama da shi, likitoci sun yi nasarar ciro almakashin tiyata da likitoci suka manta a cikinsa a tiyata ta baya. Likitocin sun manta da almakashin ne shekara 18 da suka wuce. Marar lafiyar mai suna […]
Bayan shekara 18 da yi wa wani mutumin kasar Bietnam tiyata a wani asibiti sakamakon yawan ciwon ciki da yake fama da shi, likitoci sun yi nasarar ciro almakashin tiyata da likitoci suka manta a cikinsa a tiyata ta baya.
Likitocin sun manta da almakashin ne shekara 18 da suka wuce.
Marar lafiyar mai suna Ma Ban Nhat, da yanzu yake da shekara 54, an yi masa tiyata ce bayan ya yi hadarin mota, kuma bayan bincikarsa sai aka gano an mance wani karfe a cikinsa.
Ma Ban Nhat, ya ce likitocin sun mance da almakashin ne bayan sun yi masa dinki, sai a karshen makon jiya ne aka cire masa almakashin. Hoton ciki da aka yi masa ya nuna cewa, almakashin ya kai tsawon inci 6, kuma an yi masa tiyatar awa hudu kafin a cire almakashin. Mataimakin Shugaban Gudanarwar Asibitin Gang Thep Thai Nguyen da ke da nisan mil daya a Arewacin garin Hanoi, Mista Ngo Trung Thang, ya fada wa kafar labarai ta AFP cewa, Ma Ban yana samun sauki, bayan ya kai kimanin shekara 20 yana cin abinci, yana shan abin sha tare da gudanar da harkokinsa lafiya duk da almakashin da ke cikinsa.
A cewar kafar labarai ta Suc Khoe ba Doi Song da take wallafa rahotannin ma’aikatar lafiya ta kasar Bietnam, an yi wa marar lafiyan hoton ciwon da ke damunsa ne bayan ya koka kan ciwon ciki na damunsa. A yanzu haka jami’an ma’aikatar lafiya na neman likitan da ya yi tiyatar kuma ya mance da almakashin a lardin Bac Kan a 1998. Duk da ba a gano shi ba ana ci gaba da nemansa don yin bincike game da tiyatar da ya yi.