An ciro cuta mai nauyin karamin buhun shinkafa a cikin ’yar Kenya
An cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin kilo 22 a cikinta, bayan da likitoci a kasar Kenya suka dukufa wajen yi mata tiyata. Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan cuta a jikin Esther Otieno, wadda ta fito daga kauyen Nyakatch da ke kasar Kenya.A tarihin Kenya dai […]
An cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin kilo 22 a cikinta, bayan da likitoci a kasar Kenya suka dukufa wajen yi mata tiyata. Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan cuta a jikin Esther Otieno, wadda ta fito daga kauyen Nyakatch da ke kasar Kenya.
A tarihin Kenya dai wannan shi ne karo na farko da aka taba cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin karamin buhun shinkafa daga cikinta.
An shafe kimanin wata guda kumburi na ta bullukowa daga cikin Esther, kuma ga shi tayi rauni, ba ta jin dadin komai. Bayan da aka yi aikin, yanzu ta samu walwala, tamkar matar da ta dade dauke da juna biyu, bayan ta sauka.
“Ina jin dadi, da sauki ga karfin jiki. Ubangiji ya yi amfani da mutane da dama wajen smaun lafiyata. Tun daga kan marubuci a jaridar The Standard da ta buga labarina, sai kuma masu fatan alheri a gareni da likitocin da suka yi mini tiyata,” a cewarta, lokacin da hawaye ke kwarara a idanunta, don nuna farin cikinta.
Ta ce, wannan al’amari ya auku ne alokacin da take zaune tare da masoyanta, sai kawai ’yan jaridar The Standard suka ziyarceta a Kisumu, don duba lafiyarta. A wannan lokacin tana zaune tare da masu kaunarta a rukunin gidaje na Milimani da ke Kisumu. Kuma wadannan masoya nata, suka ce ba za su bari takoma gidanta da ke kauyen Nyakach, har sai ta warke.
Shi kuwa kwararren Likita, Dokta Aggrey Akula ya jagoranci likitocin da suka yi mata tiyata,a ranar 29 ga Agustan bana.
“Tana da wani kulli ne na wata ’yar jakar ruwa a cikinta, wadda nauyinta ya fi kilo 20,kuma mun ciro ta. Abin da kawai ya rage shi ne rahoton masanin binciken kullin cutar daji, inda zai gwajin tabbatar da an cire cutar gaba daya,” inji shi.
A halin yanzu Esther na samu walwala da saukin barci, tare da aikta ayyukamn gida da suka hada da girki da wanke-wanken kayan cin abinci.
“Ba lallai ne mutum ya samu ’ya’ya ba, amma Allah na iya azurta da shi da wasu ’ya’yan da za su kula da shi. Ni ce shaida a kan haka,”injita.