An ciro kifin da ransa daga cikin hancin yaro

Likitoci sun ciro kifi da ransa daga cikin hancin wani yaro bayan da likitocin suka yi wa yaron tiyata ta awa uku. Kifin ya shige cikin hancin yaron ne lokacin da yake wanka a wani rafi da ke gonarsu, kuma abin mamaki an ciro kifin ne da ransa. Lamarin ya faru ne a gundumar Pudukkottai  […]

An ciro kifin da ransa daga cikin hancin yaro

Likitoci sun ciro kifi da ransa daga cikin hancin wani yaro bayan da likitocin suka yi wa yaron tiyata ta awa uku.

Kifin ya shige cikin hancin yaron ne lokacin da yake wanka a wani rafi da ke gonarsu, kuma abin mamaki an ciro kifin ne da ransa. Lamarin ya faru ne a gundumar Pudukkottai  da ke Jihar Tamil Nadu a kasar Indiya.

Rahoto ya ce, kifin ya shige cikin hancin matashin ne mai suna S Arul Kumar, mai shekara 12 a Unguwar Mannabelampatti kusa da Annabasal  a Pudukkottai, lokacin da yaron ya shiga wani rafi da ke kusa da gidansu tare da abokansa.

S Arul, yana cikin ruwan yana wanka ne sai ya ji wani abu ya shige cikin hancinsa,  daga bisani ya fara jin zafi a cikin hancin. Daga nan sai aka wuce da shi Babban Asibitin Annabasal da misalin karfe 10 na dare, inda likitan da ke aiki a wannan lokaci mai suna Kathiraban, ya duba cikin hancin sai ya tabbatar da cewa kifi ne ya shige cikin hancin S Arul.

Bayan tiyatar awa uku likitocin sun ciro kifin karfasa daga cikin hancin, amma zuwa wani lokaci kadan da ciro kifin ya mutu. Likitocin sun ce, da an bar kifin a cikin hanci zai iya yi wa S Arul illa.

Bayan awa daya da yin tiyatar S Arul ya dawo gida.