An ciro Kyankyaso mai tsawon inci daya daga kunnen wani mutumin Austiraliya

Wani mutumin kasar Austiraliya, ya tashi da safe yana jin zafi da radadi a cikin kunnensa na dama. Da farko ya dauka gizo-gizo ne mai ruwan guba ya fada masa cikin kunne, kuma yana ta fatan kada ya cije shi.Helmer ya yi kokarin fito da abin da ke damunsa a kunne, ta hanyar amfani da […]

An ciro Kyankyaso mai tsawon inci daya daga kunnen wani mutumin Austiraliya
An ciro Kyankyaso mai tsawon inci daya daga kunnen wani mutumin Austiraliya

Wani mutumin kasar Austiraliya, ya tashi da safe yana jin zafi da radadi a cikin kunnensa na dama. Da farko ya dauka gizo-gizo ne mai ruwan guba ya fada masa cikin kunne, kuma yana ta fatan kada ya cije shi.
Helmer ya yi kokarin fito da abin da ke damunsa a kunne, ta hanyar amfani da abin goge kunne. Da kokarinsa ya ci tura, sai ya yi ta zuba ruwa a cikin kunnen, amma duk bai yi wani tasiri ba. Helmer ya bayyana wa gidan rediyon Austiraliya irin faman da ya sha wajen fafutikar cire abin da ya shiga kunnensa.
Abokin zaman Helmer, ya yi hanzarin kai shi asibiti, inda wata likita ta zuba man zaitun a cikin kunnen. Wannan shi ma tasirinsa kadan ne, domin kyankyason ya daina yin motsi a cikin kunnen. Don haka sai likitar ta dauko matsefata ta zakulo shi daga cikin kunnen.
Ganin wannan al’amari da ya auku ga Helmer, abokinsa, sai ya fara toshe kunnensa da abin jin sauti, a duk sa’adda zai kwanta barci.